Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja a Nijeriya a ranar Litinin ta bayar da belin tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, kan kuɗin Naira miliyan 100, tare da gabatar da mutum daya da zai tsaya masa mai irin wannan adadin.
A yayin yanke hukuncin, Mai Shari’a Joyce Abdulmalik ta kafa tsauraran sharuɗɗa da dole wanda ake tuhuma ya cika kafin a kammala batun beli.
Kotun ta bayyana cewa wanda zai tsaya masa dole ne ya zama yana zaune a ko dai yankin Maitama ko Asokoro a Abuja, kuma dole ya ajiye asalin takardar mallakar fili (Certificate of Occupancy) a kotu.
Haka kuma, mai tsaya masa dole ya kasance ma’aikacin gwamnatin tarayya daga matakin Grade Level 17 zuwa sama, kuma ya gabatar da hujjar albashi na aƙalla watanni uku, wadda banki a yankin da kotun ke da iko zai tabbatar.
Kotun ta kuma umarci mai tsaya masa ya rubuta rantsuwar bayyana dukiyarsa (affidavit of means), ya sanya hannu kan sharuɗɗan beli, sannan ya miƙa hoton fasfonsa ga ofishin kotu.
A matsayin wani ɓangare na sharuɗɗan beli, El-Rufai zai ajiye dukkan fasfo dinsa na ƙasashen waje a ofishin kotu.
Kotun ta kuma umarci a kawo wasikar tabbatarwa daga sashen aikin mai tsaya masa, tare da takardar biyan haraji (tax clearance) na watanni shida da suka gabata.
Mai Shari’a Abdulmalik ta ƙara da umartar wanda ake tuhuma da ya rika zuwa hedikwatar Hukumar DSS duk ranar Jumma’ar ƙarshen kowane wata da ƙarfe 10 na safe domin sa hannu a rajista, har sai an kammala shari’ar.
Alkaliyar ta yi gargadin cewa duk wanda bai bi waɗannan sharuɗɗa ba, za a soke belin nan take.
Haka kuma kotun ta umarci wanda ake tuhuma ya gabatar da wasikar shaidar gaskiya daga Shugaban Majalisar Sarakunan Kaduna













