Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya (ICC) ta bayar da umarnin sirri don kama wasu jami’an Isra’ila guda biyar, ciki har da ’yan siyasa uku da ma’aikatan soji biyu, in ji jaridar Israeli Haaretz a ranar Lahadi.
Rahoton ya fito ne yayin da kotun da ke The Hague dama ta riga ta bayar da umarnin kama Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu a watan Nuwamban 2024 da tsohon Ministan Tsaron Isra’ila Gallant saboda laifukan yaki da laifukan da suka shafi cin zarafin bil’adama a Gaza.
Ba a samu wata sanarwa kai tsaye daga ICC game da rahoton ba. Idan an tabbatar, hakan zai sa adadin jami’an Isra’ila da kotu ke neman kamawa ya zama bakwai.
Sojojin Israeli sun kashe fiye da mutane 72,000, mafi yawansu mata da yara, kuma sun jikkata fiye da mutum 172,000 a cikin yaƙi na fiye da shekaru biyu a Gaza tun daga Oktoban 2023.
Sojojin sun ci gaba da kai hari duk da yarjejeniyar tsagaita wuta ta wucin-gadi ta fara aiki a ranar 10 Oktoban 2025; a cewar Ma’aikatar Lafiya ta Gaza, inda hakan ya yi sanadiyar mutuwar fiye da mutum 870 da jikkatar fiye da 2,540.








