| Hausa
GABAS TA TSAKIYA
2 minti karatu
Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta riƙa kai hare-hare Iran a asirce a yaƙin Amurka da Isra'ila: rahoto
Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta kai hari wata matatar mai a tsibir Lavan na Iran a farkon April, in ji majiyoyin da Wall Street Journal ta ambato, a wani abin da aka ce ɗaya ne daga cikin jerin hare-haren da Abu Dhabi ta ƙaddamar yayin yaƙin.
Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta riƙa kai hare-hare Iran a asirce a yaƙin Amurka da Isra'ila: rahoto
Wannan hoton tauraron ɗanadam ya nuna wuta na ci a kan jirage ruwa bayan wani hari kan tashar ruwan Bandar Abbas, Iran,2 ga watan Maris, 2026 / AP

Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE) ta riƙa kai hare-hare a Iran a asirce yayin yaƙin da Amurka da Isra’ila suke yi da Tehran , in ji wani rahoto da aka wallafa ranar Litinin.

Ɗaya daga cikin wuraren da ta kai hari na wata matata a tsibirin Lavan na Iran, kamar yadda wasu majiyoyi da ba a bayyana sunayensu ba suka shaida wa jaridar The Wall Street Journal.

An kai hari matatar ne a farkon watan Afrilu, daidai lokacin da Shugaban Amurka Donald Trump ke ƙoƙarin ayyana wani shirin tsagaita wuta da Iran, lamarin da ya haddasa gagarumar gobara da kuma hana matatar aiki, in ji jaridar.

Iran ta rama ta hanyar hare-haren makami mai linzami da jirage marasa matuƙa a kan Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE) da Kuwait. Ɗaya daga cikin majiyoyin ta ce Amurka ta yi maraba da shigar UAE yaƙin a asirce.

Jaridar ta ce Iran ta fi kai hari kan Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa fiye da ko wace ƙasa, ciki har da Isra’ila, inda ta ƙaddamar da hare-haren makamai masu linzami fiye da 2,800 da kuma na jirage mara matuƙa a ƙasar ta gaɓar teku.

Masu AlakaTRT Afrika - Trump ya kira martanin Iran ga shawarar zaman lafiya abin da 'ba za a lamunta ba kwata-kwata'

Hare-haren sun janyo ta’adi mai yawa a tattalin arzikin ƙasar, lamarin da ya janyo sallamar mutane da dama daga wajen aiki kuma ya "janyo muhimman sauyi a manufar ƙasar zuwa wata wadda take ganin Iran a matsayar mai aikata laifuka da ta haƙiƙance wajen zagon ƙasa ga tsarin tattalin arziki da zamantakewar ƙasar bisa ƙwarewar ‘yan ƙasashen waje da kuma mai suna wajen tsaro da zaman lafiya,"kamar yadda jami’an yankin gaɓar tekun da ba a ambato sunayensu ba suka shaida wa jaridar .

Ma’aikatar harkokin waje ta Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ba ta yi tsokaci game da hare-haren ba da jaridar ta nemi ta yi magana a kai. Sai dai kuma ta yi ishara ga wata sanarwar da ta taɓa fitarwa wadda ta jaddada ‘yancin Abu Dhabi ta mayar da martani ga matakai na gaba.

“Muhimmin abu ne a samu wata ƙasa ta Larabawa da ke gaɓar teku a matsayin abokiyar yaƙi da ta kai hari kan Iran kai tsaye,” kamar yadda Dina Esfandiary, wata mai sharhi a kan Gabas Ta Tsakiya , ta shaida wa jaridar. "Tehran yanzu za ta yi ƙoƙarin sake raba kan Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da sauran ƙasasahen Larabawa da ke gaɓar teku da ke ƙoƙarin shiga tsakani domin kawo ƙarshen yaƙin."

Rumbun Labarai
Iran ta mayar da martani ga masu shiga tsakani na Pakistan kan shawarar Amurka ta kawo ƙarshen yaƙi
Saudiyya ta musanta zargin bayar da izinin amfani da sararin samaniyarta don ayyukan soja
Iran ta harba makamai masu linzami ga sojin Amurka bayan hari kan tankar dakon manta
Darussa daga sabon tsarin tafiyar da duniya: Ba za a iya sayen tsaro ba, amma dole a gina shi
Trump ya dakatar da shirinsa na taimaka wa jiragen ruwa wucewa ta Mashigar Hormuz
Shugabannin duniya na matsa wa Iran lamba yayin da ake fargabar batun tsagaita wuta zai iya rushewa
Harin da Amurka ta kai Mashigar Hormuz ya kashe fararen-hula 5, a cewar Iran
Iran ta ce duk wani shirin Amurka kan mashigar Hormuz zai zama keta yarjejeniyar tsagaita wuta
Iran ta ba Amurka wata guda don janye toshe tashoshin ruwanta da kawo ƙarshen yaƙin Iran da Lebanon
Buɗaɗɗiyar maƙabartar Gaza: Gawawwaki 8,000 sun maƙale, yayin da aikin kwashe ɓaraguzai ya tsaya cak
Iran ta kunna na'urar tsaron sama yayin da Trump ke fuskantar wa'adin ikon shiga yaki daga Majalisa
Isra'ila na rasa goyon bayanta a tsakanin matasa 'yan  Amurka - Rahoto
Za a ci gaba da tattaunawa tsakanin Amurka da Iran ta waya – Trump
Trump ya ce bai kamata Iran ta samu makamin nukiliya ba a liyafar da aka shirya wa Sarki Charles III
Netanyahu ya bayyana a kotu don shari'ar cin hanci da rashawa a karon farko tun soma yaƙin Iran
Rikicin Gabas ta Tsakiya na koyar da darasi: Turkiyya ta zama kan gaba a zaɓin ƙasashen Afirka
Trump bai yarda da tayin Iran na sake buɗe Mashigar ruwan  Hormuz ba, in ji rahotanni
Mene ne Tehran ke gabatarwa domin kawo ƙarshen yaƙin Amurka da Isra'ila a kan Iran?
Araghchi ya faɗaɗa zirga-zirgar diflomasiyyar Iran daga Islamabad zuwa Moscow
Sisi na Masar ya yi gargaɗi kan 'ƙoƙarin da ake yi da gangan' na sake zana taswirar Gabas ta Tsakiya