Isra'ila na ci gaba da rasa goyon bayan da take samu a tsakanin matasa ‘yan Amurkawa, wani sauyi da ake ganin zai iya raunana sakamakon siyasarta na tsawon lokaci tsakaninta da ɗaya daga cikin manyan ƙawayenta, a cewar wani sabon bincike da aka yi.
Rahoton binciken wanda Cibiyar Nazarin Tsaron Ƙasa ta Isra'ila (INSS) ta fitar ya nuna yanda aka samu rarrabuwar kawuna da kuma goyon baya a tsakanin matasa Amurkawa game da Isra'ila.
Rahoton ya yi nuni kan bayanan da aka tattaro daga Cibiyar Bincike ta Amurka ta Pew Research Center a farkon watan Afrilu, wadanda suka ce kashi 60 cikin 100 na ‘yan Amurka da suka manyanta sun nuna ƙin jini ko kuma mummunan ra'ayi game da Isra'ila, yayin da a shekarar da ta gabata aka samu kusan kashi 53 cikin 100, sai kuma kashi 42 cikin 100 a shekarar 2022.
A watan Oktoban 2023 yaƙin kisan kare dangi na Isra'ila a Gaza ya soma .
Sabbin alƙaluman da aka fitar, waɗanda aka wallafa su a karon farko ta hanyar haɗin gwiwa tsakanin INSS da Cibiyar Pew da ke Washington, sun gano cewa kashi 75 cikin 100 na matasa Amurkawa masu shekaru 18 zuwa 29 suna adawa da Isra'ila. Yayin da adadin masu shekaru tsakanin 30 zuwa 4 ya kai kashi 67 cikin 100.
Binciken Pew ya kuma nuna cewa kashi 80 cikin 100 na 'yan Democrat suna da ra'ayin ƙin jinin Isra'ila, idan aka kwatanta da kashi 41 cikin 100 na 'yan Republican.
An samu masu ra’ayin ƙin jinin Isra’ila sosai a tsakanin matasan waɗanda ke goyon bayan jam’iyyar Democrat: kashi 85 cikin 100 ‘yan tsakanin shekaru 18 zuwa 29 ne, sai kuma kashi 83 cikin 100 na waɗanda ke tsakanin shekaru 30 zuwa 49.
A cewar INSS, raguwar farin jinin Isra’ila a Amurka ya bazu a cikin ƙungiyoyin addinai da yawa.
An samu rahoton rashin goyon bayan Isra’ila a tsakanin mabiya mazhabar Katolika, da Furotesta da Kiristoci masu bishara fararen fata 'yan ƙasa da shekaru 50.
Rashin farin jinin ƙasar ya fi yawa musamman a tsakanin ‘yan Katolika, inda kashi 74 cikin 100 na waɗanda ke ƙasa da shekaru 50 ke da ra'ayoyi kin jinin Isra’ila karara.
Ana kuma samun rashin goyo a tsakanin fararen fata masu bishara ‘yan wata muhimmiyar ƙungiya daga ɓangaren tushen siyasar Shugaban Amurka Donald Trump, inda kashi 50 cikin 100 ‘yan ƙasa da shekaru 50 suke da ra’ayin ƙin jinin Isra'ila, musamman idan aka kwatanta da kashi 47 cikin 100 waɗanda ke da ra'ayi mai kyau game da ƙasar.
Cibiyar INSS ta bayyana cewa masu bishara fararen fata sun kasance a kan gaba wajen goyon bayan Isra'ila baya ga al'ummar Yahudawa.
Rahoton ya kuma bayyana cewa, duk da tarihi bai nuna cewa ‘yan Katolika ba su tushen goyon bayan Isra’ila, tasirin siyasarsu yana ƙaruwa, saboda wasu alkaluma kamar Mataimakin Shugaban Amurka JD Vance da sauran muryoyin ‘yan Katolika masu ra'ayin mazan jiya waɗanda ke ƙungiyoyin kare haƙƙin Amurka masu tasowa.
A ƙarshe dai, INSS ta yi gargadin cewa waɗannan yanayin suna wakiltar wani babban ƙalubale ga babban ginshiƙin tsaron ƙasar Isra'ila. Haɗe da wasu bincike na baya-bayan nan da aka gudanar, rahoton ya nuna cewa babu wata ƙaramar al'umma daga cikin matasa Amurka da ke da ra'ayi mai kyau game da Isra'ila a halin yanzu.
Ko a tsakanin masu manyan shekaru, ra'ayoyin marasa kyau game da Isra’ila suna ƙara yawa. Idan aka ci gaba da samun haka, a cewar INSS akwai yiwuwar Isra'ila ta iya fuskantar rashin karsashi a cikin manyan jam'iyyun siyasa na Amurka.
Rahoton ya kuma jaddada cewa sauye-sauye da ake samu a cikin al'ummar Yahudawan Amurka suna ƙarfafa wannan yanayin.
A cewar INSS, al'ummar Yahudawa masu tsari - waɗanda aka daɗe ana ganin su a matsayin masu goyon bayan Isra'ila tun farko - na fuskantar raguwar tasirinsu a siyasance, tare da ƙaruwar rashin gamsuwa tsakanin Yahudawan Amurka da manufofin gwamnatin Isra'ila. Hakan na ƙara haifar da ra'ayoyi masu tsauri game da Isra'ila, musamman tsakanin matasa Yahudawa.











