Iran ta sanya wa’adin wata guda don tattaunawa kan yarjejeniyar sake buɗe Mashigar Ruwa ta Hormuz, da janye takunkumin toshe tashoshin ruwa da Amurka ta yi, da kuma kawo ƙarshen yaƙi na din-din-din a Iran da Lebanon, kamar yadda rahoton Axios na ranar Asabar ya bayyana.
Iran ta miƙa wa Amurka sabon daftarin bukatu 14 a ranar Alhamis a matsayin tsarin yarjejeniya.
Majiyoyi biyu da aka yi wa bayani kan daftarin sun ce ya ƙunshi ƙayyadadden lokaci na wata guda don cim ma yarjejeniyar da ta haɗa da ikon amfani da hanyoyin ruwa, da janye takunkumin Amurka, da kuma tsagaita wuta mai ɗorewa a dukkan ɓangarorin biyu na yaƙin.
“Idan suka yi ganganci, idan suka aikata wani abu mara kyau, amma a yanzu, za mu gani. Akwai yiwuwar hakan ta faru, tabbas,” in ji Shugaban Amurka Donald Trump lokacin da manema labarai suka tambaye shi a ranar Asabar ko zai iya ba da umarnin kai sabbin hare-hare.
A cewar majiyoyin, buƙatun za su je mataki na biyu ne kawai bayan an kammala ƙulla yarjejeniyar farko, inda za a ƙaddamar da tattaunawar ƙarin wata guda da za ta fi mayar da hankali kan shirin nukiliya.
Duk da cewa Trump ya bayyana a ranar Juma’a cewa bai gamsu da bukatar Iran ba, ya shaida wa manema labarai a ranar Asabar kafin ya bar Palm Beach zuwa Miami cewa zai duba ta yayin da yake cikin jirgi.
“Zan duba ta. Zan sanar da ku game da ita nan gaba,” in ji shi.
“Sun sanar da ni game da manufar yarjejeniyar. Za su ba ni ainihin kalmomin da aka yi amfani da su yanzu,” in ji shi.
Jim kaɗan bayan haka, Trump ya yi amfani da kakkausan harshe a dandalin Truth Social, inda ya ce “ba zai iya tunanin cewa za a amince da ita ba” kuma ya nace cewa Iran “har yanzu ba ta ɗanɗana kuɗarta yadda ya kamata ba kan abin da ta yi wa bil’adama da duniya a cikin shekaru 47 da suka gabata”.
A cikin wannan jawabi ga kafofin yada labarai, Trump ya bayyana toshe tashoshin ruwan Iran da ya yi a matsayin mataki na “mai sauƙi sosai” kuma wanda ba a fuskanci kalubale ba, inda yake ikirarin cewa hakan bai saɓa iƙirarinsa na cewa an “kawo ƙarshen” yaƙi tsakanin kasashen ba.













