| Hausa
AFIRKA
3 minti karatu
Chadi ta kama tare da korar 'yan Nijeriya da suka guje wa 'yanta'adda
Daruruwan 'yan Nijeriya da ke rayuwa a Chadi, suna neman tsira daga 'yanta'adda ne aka kama tare da korar su daga kasar a makon da ya gabata, kamar yadda wasu daga wadanda aka kama suka shaida wa AFP.
Chadi ta kama tare da korar 'yan Nijeriya da suka guje wa 'yanta'adda
'Yan Nijeriya da ke guje wa rikicin 'yan ta'adda a yankin tafkin Chadi na tsallaka wa kasashe makota don neman mafaka. / AFP

Nijeriya ta shafe shekaru 17 tana fama da rikicin ‘yanta’adda tun bayan rikicin Boko Haram da ya fara a shekarar 2009, wanda ya haifar da ƙungiyoyi daban-daban na 'yan bindiga da suka bazu a faɗin Nijar, Chadi da Kamaru.

Korar na zuwa ne a lokacin da masu nazari ke yin gargadi kan dawowar ayyukan ‘yan ta’adda a arewa maso-gabashin Nijeriya.

'Yan Najeriya biyu da aka kama a Chadi sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa an tsare kusan 'yan ƙasar 600 a kame da yawa da aka yi, kuma an jefar da su a garin Kousseri na Kamaru, wanda ke kan iyaka da babban birnin Chadi N'Djamena.

'Yan sandan Chadi sun tabbatar da cewa an kori 'yan Nijeriya amma ba su bayar da adadi ba. Sun ce sun ƙaddamar da "aikin yau da kullum" kan baƙi marasa takardu ba tare da la'akari da ƙasarsu ba.

"Jami'an tsaro sun kai sumame gidanmu a ranar Juma'a," Kyari Musa, wanda ke zaune a N'Djamena ya shaida wa AFP.

"Sun ce dukkan 'yan gudun hijirar Najeriya 'yan Boko Haram ne kuma ya kamata su bar ƙasarsu. Sun ɗauki bayananmu," in ji shi. "Sun yi gargaɗin cewa duk wanda ya dawo aka kama shi zai yi shekaru 20 a gidan yari."

A ranar Asabar, 'yan Najeriyar sun ce, jami'an kwastan na Chadi sun kai su garin Gamboru da ke kan iyakar Najeriya.

"An fara kama mutane da yawa a ranar Laraba," in ji Ari Modu, wanda ya ce shugabansa ya sallame shi daga gidan yari, kuma har yanzu yana zaune a Chadi.

An kama mutane kimanin 227 a ranar Laraba, Modu ya shaida wa AFP. Shi da Musa duk sun ce kamen na ranar Juma'a ya tara kamar mutum 371.

"'Yan sanda sun gudanar da wani bincike na mutane a cikin wani yanayi na rashin tsari, ba tare da la'akari da 'yan asalin ƙasarsu ba, waɗanda daga baya aka raka su zuwa kan iyaka," in ji Paul Manga, mataimakin babban daraktan 'yan sandan ƙasar Chadi, a tattaunawar sa da AFP. "Wannan ba farautar mutane ko cusgunawa ba ce."

Hukumomin Kamaru ba su amsa nan take ga buƙatar yin tsokaci ba.

Rikicin ‘yan ta’adda a Najeriya ya shafe shekaru yana haifar da ƙalubalen tsaro a ƙasashe maƙwabta yayin da 'yan bindiga suka bazu zuwa Nijar, Chadi da Kamaru.

Najeriya a nata ɓangaren a ‘yan shekarun nan ta yi kokarin dawo da 'yan ƙasarta daga Chadi zuwa gida.

Duk da haka, tsaffin 'yan gudun hijira da AFP ta yi hira da su a bara sun ce bayan sun koma ƙauyukansu a arewa maso gabashin Najeriya, sun sami kansu a sahun gaba na rikicin da ya ɓarke.

A cikin manyan birane masu aminci, suna fuskantar rashin aikin yi ko talauci a a yayin da ake fama da tattalin arziki mai rauni.

Wasu sun ƙare da komawa Chadi inda suka zauna kuma suka yi aiki tsawon shekaru da dma.