Maishari’a Joyce Abdulmalik ta Babbar Kotun Tarayyar Nijeriya a Abuja, ta hana hukumar zaɓe INEC amincewa da ko kuma shiga cikin ko wane babban taron da 'wani shugabanci mai cike cece-ku-ce' na Jam’iyyar ADC ya shirya.
Mai shari’ah Abdulmalik ta kuma hana tsohon shugaban majalisar dattawan Nijeriya David Mark da sauran jami’an jam’iyyar shisshigi cikin ayyuka da kuma wa’adin mulkin zaɓaɓɓun jami’an jam’iyyar a matakin jiha.
Hukuncin dai ya biyo bayan wata ƙara da Norman Obinna da saura mutum shida suka shigar a madadin shugabannin jam’iyyar ADC da kwamitocin zartarwa a matakin jiha.
Sun ƙalubalanci sahihancin wasu matakan da wani shugabanci na wucen gadi na ƙasa ya ɗauka.
Masu gabatar da ƙarar sun ce shugabancin ba shi da ikon shirya manyan tarukan jam’iyyar a matakin jiha ko kuma naɗa kwamitoci saboda yin hakan.
Sun nemi kotun ta tabbatar da wa’adin mulkinsu tare da hana gudanar da ko wane zaɓe a gefe.
A hukuncin da ta yanke, Maishari’a Abdulmalik ta ce ta gano cewa “batutuwan cikin ƙara ta farkon suna da tushe”.
Ta ce batu mafi muhimmanci shi ne ko waɗanda aka kai ƙara ta biyu da ta shida, ciki har da Mark, suna da iko a kundin tsarin mulki na iko kan zaɓaɓɓen shugabancin jam’iyyar ADC a matakin jiha, wanda wa’adin mulkinsa ke da kariya ta kundin tsarin mulki.
Ta ce, sashe na 223 na kundin tsarin mulkin shekarar 1999 ya tanadi cewa jam’iyyun siyasa za su gudanar da zaɓuka daga lokaci zuwa lokaci bisa sharaɗin dimokraɗiyya, yayin da sashi na 23 na dokokin jam’iyyar suka bayyana cewa jami’an ƙasa da na jihohin jam’iyyar za su riƙe muƙami na tsawon wa’adi bibbiyu na shekara takwas.
Saboda haka alƙaliyar ta ce “tambayar ita ce ko akwai wani laifi da Mark da sauran wadanda aka kai ƙara suka yi a lokacin da suka shirya taro kuma suka naɗa wani kwamiti mai suna kwamitin babban taro domin shirya manyan tarukan jam’iyya a matakin jiha”.
Kan batun harkokin cikin gida na jam’iyyu da waɗanda aka kai ƙarar suka tayar kuwa, ta ce “dokar ta riga ta tabbatar cewa kotuna ba za su yi katsalandan ba. Sai dai kuma inda akwai zargin ƙeta kundin tsarin mulki ko kuma doka, ya zama wajibi kotu ta shiga lamarin.”
“Inda wata jam’iyya ta yi zargin cewa an keta tsarin mulkinta, dole kotu ta yanke hukunci. Duk wata magana da ke cewa kotun ba ta da iko kan wannan bisa wannan dalilin zai gaza,” kamar yadda ta yanke hukunci.
‘Dole ɓangarori su yi biyayya ga tsarin mulkinsu’
Ta ce dole jam’iyyun siyasa su yi biyayya sau da ƙafa da tsarin mulkinsu kuma kotuna za su iya shiga lamarin inda aka ga cewa an keta tsarin mulki ko doka.
Ta ce hanyar da waɗanda aka kai ƙara suka bi ciki har da naɗa kwamitin “manyan taruka,” ta saɓa wa tsarin mulkin jam’iyyar.
Mai Shari’ar ta ce wa’adin mulkin shugabannin jam’iyyar a matakin jiha na nan kuma dole a ƙyale su su kammala shi.
Ta kuma ce waɗanda aka zaɓa kaɗai ne suke da ikon iya shirya manyan taruka a matakin jiha.
Kotun ta yi fatali da naɗin kwamitoci tare da hana hukumar zaɓe INEC amincewa da duk wani taron da suka shirya.
Kotun ta kuma hana Mark da sauran waɗanda aka kai ƙarar shirya manyan tarukan jam’iyya ba bisa tanade-tanaden tsarin mulkin jam’iyyar ba.
Alƙaliyar ta kuma hana su ɗaukar matakan da za su iya zagon ƙasa ko kuma katse ikon shugabannin jam’iyyar a matakin jiha.










