Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa tawagar masu shiga tsakaninsa ba za ta riƙa yin tafiyar sa’o’i 18 a jirgi kowane lokaci kawai don su duba takarda ba, yana mai cewa yanzu za a ci gaba da yin tattaunawa da Iran ne ta wayar tarho.
“Muna tattaunawa da su a halin yanzu, kuma ba za mu sake yin tafiyar sa’o’i 18 a jirgi ba kowane lokaci idan muna son ganin takarda. Muna yin hakan ne ta wayar tarho,” in ji Trump lokacin da yake magana da manema labarai a fadar White House ranar Laraba.
Kasashen Iran da Amurka sun gudanar da tattaunawa a babban birnin Pakistan, wato Islamabad, a ranar 11 ga watan Afrilu, sai dai ba su kai ga cimma yarjejeniyar kawo ƙarshen yaƙin da aka fara tun ranar 28 ga watan Fabrairu ba.
Wadannan shawarwari sun biyo bayan tsagaita wuta na tsawon mako biyu ne wanda Pakistan ta shiga tsakani aka amince da shi ranar 8 ga watan Afrilu. Daga baya Trump ya tsawaita lokacin tsagaita wutar, inda kuma ya soke ziyarar da wakilai na musamman, Steve Witkoff da Jared Kushner, suka shirya kaiwa Islamabad a wannan ƙarshen mako.
Trump ya amince da cewa yawancin lokaci ya fi son tattaunawa ido-da-ido.
“A koyaushe ina son zama ido-da-ido, na ɗauka hakan ya fi kyau. Amma idan ya zama dole sai ka tashi a jirgi na tsawon sa’o’i 18 duk lokacin da kake son yin zama, alhalin kuma ka riga ka san abin da tattaunawar ta ƙunsa... wannan abin ban-dariya ne,” in ji shi.
Ya sake nanata cewa duk wata yarjejeniya da za a cimma ta dogara ne akan sharadin cewa dole Iran ta yi watsi da muradunta na mallakar makamin nukiliya.
GABAS TA TSAKIYA
2 minti karatu
Za a ci gaba da tattaunawa tsakanin Amurka da Iran ta waya – Trump
Shugaba Donald Trump ya sanar da cewa tattaunawar da ake yi yanzu tsakanin Amurka da Iran ana yin ta ne ta waya.

Rumbun Labarai








