Rundunar kare juyin juya halin Iran (IRGC) ta yi gargaɗi ranar Laraba cewa duk wani sabon hari na Amurka da Isra’ila zai iya janyo wani rikici mai faɗi da zai iya wuce yankin.
A wata sanarwar da kamfanin dillancin labaran Tasnim ya ɗauka, rundunar IRGC ta ce Amurka da Isra’ila sun gaza koyan darasi daga abin da ta bayyana a matsayin shan kaye na dabaru a-kai-a-kai daga hannun Iran.
Rundunar ta yi iƙirarin cewa duk da hare-haren da aka kai da “dukkan ikon soji biyun da suka fi tsada a duniya ,” Iran ba ta gama amfani da dukkan ikonta a kan abokan gaba ba .
“Idan aka ci gaba da maimaita tsangwama a kan Iran, yaƙin na yanki da aka yi alƙawarinsa a wannan karon zai bazu fiye da yankin,” in ji sanarwar.
Rundunar IRGC ta kuma yi gargaɗin “hare-hare na murƙushewa” a wuraren [da] “ba za ku iya zata ba.”
“Mu mazajen yaƙi ne, kuma za ku ga ƙarfinmu a fagen daga , ba wai a sanarwa na banza kawai ko kuma shafukan intanet ba,” in ji sanarwar.
Shugaban Donald Trump ya bayyana ranar Litinin cewa shi ya ɗaga kai hari kan Iran ne bisa buƙatar shugabannin ƙasashen Larabawa na gaɓar teku.
Pakistan ta ce tana aiki domin farfaɗo da tattaunawar diflomasiyar da ta ci tura tsakanin Iran da Amurka, biyo bayan wata yarjejeniyar tsagaita wuta da Pakistan ta samar ranar 8 ga watan Afrilu.
Amurka da Isra’ila sun ƙaddamar da hare-hare kan Iran ranar 28 ga watan Fabrairu, lamarin da ya janyo hare-haren ramuwar gayya daga Tehran a kan Isra’ila da kayayyakin Amurka a yankin , tare da rufe mashigin ruwan Hormuz.













