| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
NDLEA ta tarwatsa ƙungiyar masu hada miyagun ƙwayoyi ta Nijeriya da Mexico ta kama mutum 10
Shugaban hukumar, Mohamed Buba Marwa ya bayyana hakan a hedikwatar hukumar da ke Abuja, inda ya ce wannan aiki ya yi wa manyan ƙungiyoyin aikata laifukan ƙetare iyaka mummunar illa.
NDLEA ta tarwatsa ƙungiyar masu hada miyagun ƙwayoyi ta Nijeriya da Mexico ta kama mutum 10
Buba Marwa Shugaban NDLEA ya ce kamen ya yi wa gungun mummunar illa / Nigeria NDLEA

Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Nijeriya, NDLEA ta tarwatsa wata babbar ƙungiya ta masu haƙa da samar da miyagun ƙwayoyi ta methamphetamine da aka bayyana a matsayin mafi girma da aka taɓa ganowa a Najeriya.

Hukumar ta kama wani shahararren shugaban ƙungiyar, ’yan Mexico uku da kuma ’yan Nijeriya shida yayin wani gagarumin samame da aka gudanar a jihohin Ogun da Lagos.

Shugaban hukumar, Mohamed Buba Marwa ya bayyana hakan a hedikwatar hukumar da ke Abuja, inda ya ce wannan aiki ya yi wa manyan ƙungiyoyin aikata laifukan ƙetare iyaka mummunar illa.

Ya ce an gudanar da aikin ne bayan shafe watanni ana tattara bayanan sirri, inda jami’an sashen musamman na hukumar suka kai samame a wani dakin samar da methamphetamine da ke ɓoye a cikin dajin Abidagba, cikin ƙaramar hukumar Ijebu ta Gabas a jihar Ogun, inda aka kama masu laifin suna sarrafa miyagun ƙwayoyi a matakin masana’antu.

Daga cikin waɗanda aka kama a dajin akwai ’yan Nijeriya huɗu da kuma ’yan Mexico uku da ake zargin an shigo da su Nijeriya domin su taimaka wajen fasahar samar da wannan muguwar ƙwaya.

Marwa ya ƙara da cewa wani rukuni na jami’an tsaro sun kuma kai farmaki gidan shugaban ƙungiyar da ke Lekki a jihar Lagos, inda aka bayyana shi da sunan Anochili Innocent, wanda ake zargi da kasancewa jagoran ƙungiyar.

A yayin farmakin, an ce jami’an sun gano fasfo da wayoyin hannu na ’yan Mexico da aka kama, abin da ya ƙara tabbatar da alaƙarsa da shigo da su da kuma tafiyar da aikin ƙungiyar.

Hukumar ta bayyana cewa bayan wannan farmaki, an kuma kama wasu mutum biyu tare da gano wani gidan da ake amfani da shi wajen ɓoye kayan miyagun ƙwayoyi.

Jimillar abin da aka kama ya kai kilo 2,419 na methamphetamine da sinadarai masu haɗari, wanda darajarsa ta kai kusan dala miliyan 362.9, wato sama da Naira biliyan 480.

A ƙarshe, Marwa ya yi gargaɗi cewa Nijeriya za ta ci gaba da zama ƙasa mai tsauri ga masu safarar miyagun ƙwayoyi, inda ya jaddada cewa hukumar ba za ta daina bin sawunsu ba har sai ta tarwatsa dukkanin ƙungiyoyin da ke wannan aiki.

Ya kuma yi kira ga ’yan Nijeriya da su riƙa ba da rahoton duk wani abin da suke zargi domin taimakawa yaƙin da ake yi da miyagun ƙwayoyi.

Rumbun Labarai
Babbar Kotun Tarayya a Abuja Nijeriya ta ba da belin Nasir El-Rufai kan naira miliyan 100
Nasarori da jayayya da mamaki sun karaɗe zaɓukan fid da gwani na Majalisar Wakilan APC a Nijeriya
Nijeriya ta tsananta sa ido bayan WHO ta ayyana dokar ta-baci kan Ebola da ta kashe mutum 88 a Congo
Rundunar 'yansandan Nijeriya ta tabbatar da kashe jami'anta 17 a harin ta'addanci a Jihar Yobe
'Yanbindiga a Nijeriya sun sace ɗaliban da ba a san adadinsu ba a Jihar Borno
Dakarun Amurka da na Nijeriya sun kashe mataimakin shugaban Daesh, Abu-Bilal al-Minuki: Trump
An sallami 'yansandan Nijeriya biyar kan zargin fashi da makami a Jihar Ribas
Tinubu ya yi gargaɗi kan siyasar ‘a-mutu-ko-a-yi-rai’ a zaɓukan fid da gwani na Jam'iyyar APC
Nijeriya ta buƙaci shiga Hukumar Makamashi ta Duniya a IEA a matsayin memba
'Yanta'addan Lakurawa sun kashe jami'an hukumar kwastam biyu a Jihar Kebbi ta Nijeriya
Rundunar sojin Nijeriya ta ce babu shaida ta kashe fararen-hula a harin sama a kasuwa a Zamfara
Nijeriya na tattaunawa da Bankin Duniya kan sabon bashin $1.25bn: rahoto
Shugaba Tinubu na Nijeriya na halartar taron Afirka da Faransa a Kenya
Rundunar Sojin Nijeriya ta musanta kashe fararen-hula a harin sama a jihar Neja
Nijeriya da Amurka sun ƙarfafa haɗin gwiwa kan tsaro da yaƙi da ta’addanci bayan ganawa a Washington
Sojin Nijeriya sun halaka ‘yanta’adda 50, sun yi asarar dakaru biyu yayin daƙile harin ISWAP a Yobe
'Yanbindiga a Nijeriya sun kashe mata masu juna biyu uku da wasu mutum 11 a Filato
Dakarun sojin Nijeriya sun kashe 'yanta'addan ISWAP da masu garkuwa da mutane
Sojojin Nijeriya sun ceto yaran da aka sace daga gidan marayu
Sanƙarau ta kashe mutum 33 a Sokoto yayin da hukumomi ke ƙoƙarin daƙile yaɗuwarta