Rundunar sojin Nijeriya a ranar Laraba ta ce babu wata shaida mai gamsarwa da ke nuna an samu asarar fararen-hula sakamakon harin jirgin sama kan 'yanta'adda a jihar Zamfara a wannan watan.
Ta ce ba a tabbatar da rahotannin da ke nuna adadi mai yawa na mutanen da suka mutu ba kuma suna iya zama masu ruɗani.
A farkon wannan makon ne ƙungiyar kare hakkin ɗan’adam ta Amnesty International ta ce a kalla fararen-hula 100 ne aka kashe a harin jirgin sama na 10 ga Mayu a wata kasuwa mai cunkoso a garin Tumfa, tana kira ga hukumomi da su buɗe bincike cikin gaggawa.
Mai magana da yawun Hedkwatar Tsaro, Manjo Janar Michael Onoja, ya ce a cikin wata sanarwa: "Babu wata shaida mai gamsarwa kuma wacce aka tabbatar da ita game da asarar fararen-hula ta kowane bincike na hukuma ko tantancewa mai zaman kansa."
Ya ce an gudanar da harin ne bisa dokokin jinƙai na ƙasa da ƙasa kuma an nufi wani 'taron manyan shugabannin 'yanta'adda ne da aka tabbatar' a ƙauyen, wanda aka gina kan bayanan leƙen asiri daga mabambantan kafofi.
Onoja ya ƙara da cewa yanayin harin ya sa tantance asarar cikin gaggawa ya yi wahala, amma binciken da aka gudanar bayan harin ya nuna cewa "an kawar da wasu 'yanta'adda."
A yanzu ana yawan amfani da jiragen yaƙi marasa matuƙa wajen kai wa ‘yanbindiga hari a cikin dazuzzuka da surƙuƙin da suke ɓuya.









