| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
'Yanbindiga a Nijeriya sun kashe mata masu juna biyu uku da wasu mutum 11 a Filato
Rahotanni sun ce maharan sun kutsa cikin al’ummar ne da tsakar dare yayin da jama’a suke barci inda suka rinƙa bi gida-gida suna kai hari ga mutanen da ba su ji ba su gani ba.
'Yanbindiga a Nijeriya sun kashe mata masu juna biyu uku da wasu mutum 11 a Filato
Yadda mutane suka taru washe garin harin da 'yanbindiga suka kai cikin dare a Angwan Rukuba da ke Jihar Filato a ranar 30 ga Maris na 2026. / Reuters

An kashe aƙalla mutum 14, ciki har da mata masu juna biyu guda uku, a wani hari da ‘yanbindiga suka kai da tsakar dare a kan al’ummar Ngbra Zongo da ke Gundumar Kwall a Ƙaramar Hukumar Bassa ta Jihar Filato da ke Nijeriya, kamar yadda mazauna yankin suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu a ranar Juma’a.

Rahotanni sun ce maharan sun kutsa cikin al’ummar ne da tsakar dare yayin da jama’a suke barci, inda suka rika harbe-harbe kan mai uwa-da-wabi, lamarin da ya tilasta wa mutane da dama tserewa daga gidajensu.

Jihar Filato ta sha fama da tashe-tashen hankula masu alaƙa da rikicin manoma da makiyaya, rikice-rikicen ƙabilanci, da hare-haren ramuwar gayya waɗanda suka yi sanadin mutuwar ɗaruruwan mutane a shekarun baya-bayan nan.

Da yake magana kan lamarin, wani mazaunin yankin mai suna Raphael Ebi, wanda ya tsira ta hanyar guduwa cikin daji, ya shaida wa Anadolu cewa maharan sun shiga al’ummar da misalin ƙarfe 12 na dare ranar Juma’a sannan suka fara harbe-harbe ba kakkautawa.

“Sun rika bi daga gida zuwa gida suna kai hari ga mutanen da ba su ji ba su gani ba,” in ji shi.

Wani mazaunin yankin, Chigoji Ameh, ya ce mata masu juna biyu uku na cikin waɗanda aka kashe a harin, yayin da wasu da dama suka jikkata.

Sakatare Janar na Ƙungiyar Ci gaban Al’umma, Danjuma Auta, ya yi Allah wadai da harin, yana mai bayyana shi a matsayin “abin takaici kuma wanda ba za a amince da shi ba.”

“Mun yi matuƙar baƙin ciki da wannan ci gaba da zubar da jini a al’ummominmu,” in ji Auta. “Dole ne hukumomin tsaro su ƙara ƙaimi wajen kare al’ummomin karkara tare da tabbatar da kama waɗanda ke da hannu a waɗannan hare-hare tare da gurfanar da su gaban shari’a.”

Yayin da hukumomi ba su fitar da wata sanarwa a hukumance ba game da harin har zuwa yammacin ranar Jumma’a, wasu majiyoyin tsaro sun shaida wa Anadolu cewa an tura jami’an ‘yansanda zuwa yankin da abin ya faru.

Mai magana da yawun Rundunar ‘Yansandan Jihar Filato, SP Alabo Alfred, ya shaida wa Anadolu cewa “an shawo kan lamarin. Jami’anmu na aiki tare da mazauna yankin da abin ya shafa.”