A ranar Asabar, Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya sake jaddada cikakken goyon bayan Ankara ga 'yancin kai da tsaron Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) a yayin wata tattaunawar waya da Shugaban UAE Mohamed bin Zayed Al Nahyan, yayin da tashin hankali ke ci gaba a fadin yankin.
Shugaba Erdogan ya kuma mika fatan samun gaggauta farfadowa daga barnar da rikicin yankin ke haddasawa, kuma shugabannin biyu sun tattauna dangantaka tsakaninsu da ci gaban yankin da na duniya, in ji Daraktan Sadarwa na Turkiyya a dandalin sada zumunta na Turkiyya, NSosyal.
A lokacin kiran, Erdogan ya ce Turkiyya na ba da muhimmanci wajen karfafa haɗin gwiwa da UAE a fannoni da dama, musamman ciniki, makamashi da tsaro.
Idan za a duba rikicin Amurka da Iran da ke gudana, Erdogan ya bayyana abubuwan da ke faruwa a yankin a matsayin abin takaici kuma ya ce Turkiyya na ci gaba da tuntuɓar kasashen da abin ya shafa domin taimakawa samo mafita ta diflomasiyya tsakanin Washington da Tehran.
Ya kuma jaddada cewa ana buƙatar ƙarin tattaunawa da haɗin gwiwa don magance kalubalen tsaro na yankin, a cewar daraktan.

















