Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya bayyana ranar Litinin cewa shi ba zai yi murabus ba kuma ya ce zai shigar da ƙara domin ƙalubalantar shirin tsige shi game da badaƙalar zargin satar dala miliyan huɗu.
“Yayin da muka ga wasu kiraye-kiraye na neman na ajiye aiki, babau wani abu a cikin hukuncin kotun tsarin mulki da ya tilasta mini na ajiye muƙami na,” kamar yadda Ramaphosa ya bayyana a wani jawabin da ya yi a talabijin ga ‘yan ƙasar.
Lamarin ya sake fitowa ne a makon da ya gabata bayan kotun ta juya hukuncin watsi da wani rahoton majalisar dokoki na shekarar 2022 da ya ce Ramaphosa "ta yiwu ya aikata" babban ƙeta doka da rashin ɗa’a.
An zargi Shugaban ƙasar mai shekara 73 da laifin ɓoyewa daga ‘yansanda da hukumomin haraji wani kutse da satan kuɗaɗen ƙetare na shekarar 2020 da aka yi zargin cewa an ɓoye a cikin kujeru da gadaje a gidan gonarsa na alfarma a lardin arewaci na Limpopo.
A wani jawabi da ya yi bisa talabijin , Ramaphosa ya ce babu wani abu a hukuncin ranar Juma’a na kotun tsarin mulki da ya isa hujja ga tsige shi ko kuma cire shi daga muƙaminsa.
Rahoton Majalisar dokoki “na da rauni”
"Sabida haka bisa girmamawa ina so na bayyana cewa ba za ni ajiye aiki na ba," in ji shi , yana mai ƙarawa da cewa idan ya yi hakan, zai "ba da gaskatawa" ga rahoton majalisar dokoki "mai rauni" ne.
"Ina nan ba za ni ajiye aiki ba," in ji shi.
Wani kwamiti mai zaman kansa ya ce Ramaphosa "zai yiwu ya aikata " wasu jerin ƙeta doka masu muni da rashin ɗa’a dagane da kutsen.
Amma majalisar dokoki ,wadda a wancan lokacin jam’iyyarsa ta ANC ce ke jagorantarta, ta ƙi a shekarar 2022 ta buɗe shirin tsige da zai iya tilasta masa barin mulkin ƙasar.
Kotun tsarin mulkin ya ba da umarnin cewa a tura rahoton kwamitin zuwa wani kwamiti na tsige shi, a matsayin wani martani ga ƙorafin da jam’iyyar EFF mai rajin neman daidaito na tattalin arziki ya shigar.
Zaɓuka masu zuwa
Jam’iyyar ANC tana rasa goyon baya game da alƙawurran manufofi da ba ta cika ba da kuma zarge-zargen da ake ta yi mata na cin hanci da rashawa da raunin mulki, gabannin zaɓukan ƙananan hukumomi da za a yi ranar 4 ga watan Nuwamba.
Ramaphosa, wanda ofishinsa ya bayyana a makon da ya gabata cewa ta "lura" kuma ta girmama hukuncin kotun, ya bayyana a jawabinsa cewa an ba shi shawarar neman ƙarin haske na shari’a game da rahoton kwamitin.
Zai yi nazari game da yiwuwar "kuskure kan aikata muhimman kura-kurai, da kuma cim ma matsaya da ba ta da tushe bisa gaskiya", in ji shi.
Ramaphosa, wani tsohon mai gwagwarmayar yaƙi da mulkin wariyar launin fata wanda ya zama ɗankasuwa kafin ya shiga siyasa, ya musanta aikata ba daidai ba a badaƙalar.
Ya ce lallai an yi kusten, amma ya musanta iƙirarin wani toshon shugaban hukumar leƙen aisri cewa shi ya sa a saci ɓarayin a wani ƙoƙari na rufa-rufa kan batun.
Ya ce shi ya ba da rahoto game da kutsen ga ‘yansanda kuma ya bayyana cewa kuɗin ya samu ne daga sayar da ɓauna 20 kan kuɗi $580,000.













