Wani harin jirgin sama mara matuƙi da dakarun sa-kai suka ƙaddamar ya fada gidan iyayen wani kwamanda mai mara wa rundunar sojin ƙasar baya, inda ya kashe danginsa tara, kamar yadda majiyoyi biyu suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP a ranar Lahadi.
Majiyoyin sun ce harin, wanda ya auku da misalin ƙarfe 10:00 na dare agogon yankin a ranar Asabar, ya fada gidan iyayen Abu Aqla Kaykal, kwamandan rundunar Sudan Shield Forces, a ƙauyen Al Kaheli, kimanin kilomita 40 gabas da Wad Madani, babban birnin Jihar Al Jazirah da ke tsakiyar Sudan.
Sun ɗora alhakin harin kan dakarun sa-kai na RSF, waɗanda ke yaƙi da rundunar sojin Sudan tun watan Afrilun 2023.
Daga cikin waɗanda aka kashe har da ƙannen Kaykal guda biyu, Azzam da Haidar, da wani ɗan’uwansa, Siddiq Bakhit – wanda kwamanda ne a rundunar Sudan Shield Forces – da kuma ƙananan yara shida na gidan, in ji majiyoyin. Sun ƙara da cewa gidan da kuma wasu gidaje masu maƙwabtaka da su sun lalace.
Mummunan yaƙi
Kaykal ya taɓa yin aiki a matsayin kwamandan RSF a jihar Al Jazirah.
Ya sauya sheka zuwa ɓangaren rundunar soji ne a watan Oktoban 2024, bayan nan mayakansa suka bi sahun rundunar soji a farmakin da ya taimaka wa sojojin ƙasar sake ƙwace muhimman yankuna a tsakiyar Sudan, ciki har da Al Jazirah da kuma babban birnin ƙasar, Khartoum.
Yanzu haka yaƙin Sudan, wanda ya shiga shekara ta huɗu, ya kashe dubban mutane – inda wasu kiyasin ke nuna cewa adadin waɗanda suka mutu ya haura 200,000 – ya raba miliyoyin mutane da gidajensu, sannan ya janyo ɗaya daga cikin mafi girman matsalar jin ƙai a duniya.
AFIRKA
2 minti karatu
Harin jirgi mara matuƙi a Sudan ya kashe ’yan’uwa tara na wani kwamandan da ke mara wa soji baya
Wani harin jirgi mara matuƙi da dakarun sa-kai suka ƙaddamar ya fada gidan iyayen wani kwamanda mai mara wa rundunar sojin ƙasar baya, inda ya kashe danginsa tara, kamar yadda majiyoyi biyu suka shaida wa AFP a ranar Lahadi.

Rumbun Labarai








