Yayin da farashin mai ke hauhawa kuma kan famfunan gidajen mai ke ƙafewa a faɗin Afirka da sauran wurare, Kenya ta ɗage dokar hana shigo da abin da ake kira "man fetur mai datti", tana mai nuni da buƙatar ci gaba da aiki da kayayyaki a lokacin ƙarancin mai da yaƙin Gabas ta Tsakiya ya haifar.
Umarnin ya fara aiki a makon da ya gabata kuma zai yi aiki na tsawon watanni shida a matsayin wani ɓangare na matakan gaggawa ga ƙasar da ta dogara sosai kan shigo da mai daga Yankin Gulf. Zai ba da damar shigo da mai dauke da matsakaicin sulfur na 50mg/kg.
Ko da yake an dauki matakin ne don magance ƙarancin mai, shawarar ta zo ne wata guda bayan gwamnati ta ƙi jigilar mai da aka ruwaito yana ɗauke da dattin sulfur mai yawan 43mg/kg, wanda hakan ya haifar da me ka iya zuwa ya dawo a tsakanin jama'a.
A lokacin, manyan jami'ai a ɓangaren makamashi na Kenya, ciki har da shugaban bututun mai na ƙasa da kuma shugaban hukumar kula da makamashi, suka yi murabus bayan zargin rashin daidaito a cikin sarkakiyar samar da mai ta Kenya.
Sulfur wani sinadarin datti ne da ke faruwa a zahiri wanda ke cikin ɗanyen mai da iskar gas lokacin da aka fitar da su daga ƙarƙashin ƙasa.
Lalata Injina
Idan man fetur mai ɗauke da sulfur ya kone a cikin inji, yana samar da dattin hayakin sulfur wanda za su iya haifar da gurɓatacciyar iska da lalacewar injin.
Saboda haka, masu fafutukar kare muhalli da ƙungiyoyin kare masu amfani da kayayyaki a Kenya sun yi gargaɗin cewa ƙaruwar sinadarin sulfur a cikin mai a lokacin da aka yi watsi da shi yana haifar da hatsari ga muhalli, lafiyar ɗan adam da injina.
"Ba za a ga ainihin tasirin wannan shawarar a bakin famfon mai ba; za a gan ta ne a yawaitar zuwa asibiti, a cikin yawan kamu wa da asma da cututtukan huhu na yau da kullum, da kuma daidaituwar ingancin iska," in ji Peter Ngare, ƙwararren masani kan harkokin sadarwa na sauyin yanayi a tattaunawar sa da TRT Afrika.
"Karancin mai na iya gurgunta tattalin arziki, kawo cikas ga sufuri da kuma haifar da hauhawar farashin kaya. Amma bai kamata a taɓa tsara zaɓin a matsayin zaɓi tsakanin samuwa da aminci ba. Wannan zaɓi ne na ƙarya."
Datti mai yawa har ninki biyar
Ƙungiyar Masu Amfani da Kaya ta Kenya (Cofek), wadda ke fafutukar kare haƙƙin masu amfani da Kaya ta Kenya, ta ce ta "damu matuka" domin rage yawan sinadarin sulfur daga 10mg/kg zuwa 50mg/kg - ƙarin ninki biyar - kuma yana mayar da ingancin man fetur na Kenya zuwa inda yake a shekarar 2015.
"Wannan ba gyara ba ne na fasaha. Matsalar haƙƙin masu amfani ce," Stephen Mutoro, babban sakataren Cofek ya fada wa TRT Afrika.
Ya ce ƙungiyar tana sake duba tushen shari'a na sassaucin da nufin shigar da ƙara kan kundin tsarin mulki cikin gaggawa.
Yaƙin da Amurka da Isra'ila ke ci gaba da yi kan Iran da kuma ɗaukar fansar Tehran ya bar gwamnatoci a faɗin duniya suna fafutukar rage ƙarancin mai, hauhawar farashin mai da kuma katsewar hanyoyin samar da kayayyaki sakamakon rufe Mashigar Teku ta Hormuz, hanyar da ke ɗauke da kusan kashi ɗaya bisa biyar na man fetur da iskar gas na duniya.
Ƙasashen Afirka da dama waɗanda suka dogara sosai kan shigo da mai daga ƙasashen waje ta Mashigar Hormuz na daukan matakai don kare tattalin arzikinsu.
Habasha ta sanya tsarin raba mai wanda ke ba da fifiko ga sufuri na jama'a, noma, masana'antu da muhimman ayyukan gwamnati. Sudan ta Kudu ta gabatar da rabon wutar lantarki a babban birnin Juba, don adana man dizal, yayin da Tanzania ta ƙara farashin mai a duk faɗin ƙasar da kusan kashi ɗaya bisa uku.
Kenya ta riga ta kulla yarjejeniyar shigo da mai daga Gwamnati zuwa Gwamnati (G2G) da ƙasashen Gulf, wanda aka gabatar a shekarar 2023, wanda ya ba ta damar shigo da mai mai tsafta akan bashi da kuma rage masu shiga tsakani. Masu samar da mai a ƙarƙashin yarjejeniyar sun haɗa da kamfanin mai na Saudiyya Aramco da kamfanin mai na Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), Adnoc.
Duk da haka, shugabannin 'yan adawa da masu suka sun yi tambaya game da dalilin da ya sa yarjejeniyar ta gaza magance matsalar ga ƙarfin tattalin arzikin Gabashin Afirka a rikicin da ake ciki a yanzu.
"An yi tsammanin tsarin shigo da mai tsakanin Gwamnati da Gwamnati zai kare Kenya daga irin wannan matsalar samar da mai. Madadin haka, Kenya yanzu tana da man fetur mafi tsada a Gabashin Afirka, kuma damuwa ta farko ta tsarin ta haifar da matsalar inganci, badakalar saye da kuma koma baya ga dokoki," in ji Mutoro.
Kare matakin da aka dauka
Ba da izinin amfani da man fetur "mai datti" a cikin kasuwar cikin gida yana nufin cewa masu ababen hawa za su cika tankunan su da mai wanda zai iya lalata injina, tare da farashin da ya wuce sulai din Kenya 200,000 ($1,550) a wasu sassa kawai, in ji jami'in Cofek.
Duk da haka, gwamnatin Kenya ta kare shawararta, wanda ta ce an ɗauka bayan tattaunawa mai zurfi.
Ma'aikatar Zuba Jari, Kasuwanci da Masana'antu ta Kenya ta ce an ɗauki matakin ne bayan ta "sami buƙatu daga masu ruwa da tsaki a fannin man fetur, ciki har da Ma'aikatar Makamashi da Man Fetur, game da ƙalubalen samun mai wanda ya cika matakan bin ƙa'ida na yanzu".
Ma'aikatar ta ce an amince da wannan sassaucin "ƙarƙashin jagorancin Majalisar Ma'aunin Ƙasa", wacce ita ce hukumar da ke da alhakin tabbatar da ingancin kayayyaki da ayyuka a ƙasar da ke Gabashin Afirka, kuma an ɗauki matakin ne bisa la'akari da buƙatar kare lafiyar masu amfani da man fetur na Kenya da kuma kwanciyar hankalin tattalin arziki".
Matakin "na ɗan lokaci" na da manufar tabbatar da ci gaba da wadatar mai da kuma ci gaba da dorewar tattalin arziki a lokacin da ake fama da matsalar karancin mai a duniya. Za a sake duba matakin a ƙarshen watanni shida,'' in ji shi a cikin wata sanarwa a ranar 30 ga Afrilu.
Duk da haka, a cewar Mutoro, watsi da matakan sulfur matsala ce da ta wuce iyakokin Kenya, yana mai cewa manufar ta saba wa yarjejeniyar yanki da aka gabatar a shekarar 2015 kan ƙa'idodin mai a Gabashin Afirka.
"Ka'idojin ingancin mai na Gabashin Afirka (EAC) ba ƙa'idojin gudanarwa na cikin gida ba ne wanda minista a majalisar ministoci zai iya watsi da su da sanarwar manema labarai. Su ne sakamakon tsarin daidaito na yanki a ƙarƙashin Yarjejeniyar EAC, wanda Kenya ta sanya hannu a kai," in ji Mutoro.
"Dakatar da ƙa'idojin da EAC ta amince da su na tsawon watanni shida ba tare da la'akari da Majalisar EAC ko ƙasashen da ke haɗin gwiwa ba batu ne na bin ƙa'idoji na yarjejeniya, ba kawai batun manufofin cikin gida ba," in ji shi.
‘Tarabbabi’
Masana muhalli sun kuma yi gargaɗi game da tasirin da barin "mai datti" ya koma kasuwar cikin gida, suna cewa tasirin zai wuce lokacin da aka kayyade amfani da shi na watanni shidada.
"Muna magana ne game da dubban motoci da ake amfani da su da ke amfani da wannan man fetur mai ƙarancin inganci, wanda gurɓataccen sinadarin sulfur ya lalata. Fitar da wannan hayaki ya isa hatsari ko da na kwana ɗaya, balle watanni shida, a ƙasar da aka daɗe ana cewa ita ce jagorar duniya a fannin kiyaye muhalli. Wannan abin mamaki ne," in ji mai fafutukar kare muhalli James Wakibia.











