| Hausa
DUNIYA
3 minti karatu
Amurka ta amince a sayar wa Isra’ila, UAE, Kuwait, Qatar makaman da suka haura na dala biliyan 8.6
Wannan sanarwa tana zuwa ne yayin da yaƙin Amurka da Isra’ila da Iran ya cika mako tara da farawa, kuma sama da mako uku tun bayan da aka fara aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta mai cike da rauni.
Amurka ta amince a sayar wa Isra’ila, UAE, Kuwait, Qatar makaman da suka haura na dala biliyan 8.6
Iran ta kai hari UAE da akalla makamai masu linzami 2,000 da jirage marasa matuka, inda ta yi mummunan ta’adi yayin yakin kwanaki 40. / AP / AP

Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta amince da sayar da kayan aikin soja na dala biliyan 8.6 ga ƙawayenta na Gabas ta Tsakiya da suka haɗa da Isra’ila, da Qatar, da Kuwait, da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE).

Sanarwar da Ma’aikatar Harkokin Wajen ta fitar a ranar Juma’a ta zo ne yayin da yaƙin Amurka da Isra’ila da Iran ya cika mako tara, kuma mako uku bayan tsagaita wuta mai rauni wanda ƙasar Pakistan ta shiga tsakani ta fara aiki.

Sanarwar Ma’aikatar Wajen ta haɗa da amincewa da sayar wa Qatar tsarin kariya daga hare-haren sama na Patriot da sabis na makamai masu linzami akan kuɗi dala biliyan 4.01, da kuma makamai masu linzami na Advanced Precision Kill Weapon Systems (APKWS) akan dala miliyan 992.4.

Haka kuma, an amince da sayar wa Kuwait tsarin haɗin gwiwa na sarrafa yaƙi (integrated battle command system) akan dala biliyan 2.5, sannan an amince a sayar wa Isra’ila makaman APKWS akan dala miliyan 992.4.

Ma’aikatar Harkokin Wajen ta kuma amince da sayar wa UAE makaman APKWS a kan dala miliyan 147.6.

Babban kamfanin da zai samar da makaman APKWS ga Qatar, Isra’ila, da UAE shi ne BAE Systems, kamar yadda Ma’aikatar Harkokin Wajen ta bayyana.

Kamfanonin RTX da Lockheed Martin ne manyan ’yan kwangilar da za su samar da tsarin sarrafa yaƙi ga Kuwait da kuma makaman Patriot ga Qatar, in ji Ma’aikatar.

Kazalika kamfanin Northrop Grumman ma yana ɗaya daga cikin manyan ’yan kwangilar a yarjejeniyar ta ƙasar Kuwait.

Yaƙi ya tsaya na ɗan lokaci

Amurka da Isra’ila sun fara kai wa Iran hari ne a ranar 28 ga Fabrairu, lamarin da ya janyo mayar da martani daga Iran kan ƙawayen Amurka da ke yankin Tekun Fasha da kuma rufe mashigar ruwa ta Hormuz.

An dakatar da yaƙin tun ranar 8 ga Afrilu, inda aka gudanar da tattaunawa kai tsaye sau ɗaya kawai wadda ba ta yi nasara ba.

Shugaban Amurka Donald Trump, wanda ke fuskantar matsin lamba a gida don neman izinin majalisa kan yaƙin, ya rubuta wa ’yan majalisa wasiƙa a ranar Juma’a da yamma yana bayyana cewa an “kawo ƙarshen” gaba — duk da cewa babu wani canji a yanayin dakarun Amurka.

Iran ta ci gaba da ikon mallakar mashigar Hormuz, inda ta toshe hanyoyin samar da mai, iskar gas, da takin zamani, yayin da Amurka kuma ta saka takunkumin toshe tashoshin jiragen ruwa na Iran.

Trump ya kuma bayyana a ranar Juma’a cewa “bai gamsu ba” da sabon shawarar sulhu da Iran ta gabatar.

Kamfanin dillancin labaran IRNA ya ruwaito cewa Iran ta miƙa takardar shawarar ga mai shiga tsakani, wato Pakistan, a ranar Alhamis da yamma, ba tare da bayyana dalla-dalla kan abin da takardar ta ƙunsa ba.