| Hausa
AFIRKA
3 minti karatu
Ghana ta ƙi karɓar tallafin lafiya na Amurka na dala miliyan 109 bisa damuwa kan tsaron bayanai
Kamfanin dillancin labaran Reuters ya ruwaito ranar Talata 28 ga watan Afrilu cewa gwamnatin Shugaba John Mahama ta ƙi amincewa da sharaɗin shirin na miƙa muhimman bayanai na kiwon lafiya na ƙasar.
Ghana ta ƙi karɓar tallafin lafiya na Amurka na dala miliyan 109 bisa damuwa kan tsaron bayanai
Shugaban Ghana John Dramani Mahama / Reuters

Ghana ta ƙi ci gaba da wata yarjejeniya ta tallafin kiwon lafiya tsakaninta da Amurka, lamarin da ya kawo koma baya ga ƙoƙarin Shugaba Donald Trump na kawo gyara ga shirin tallafin ƙetare na gwamnatinsa

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya ruwaito ranar Talata 28 ga watan Afrilu cewa gwamnatin Shugaba John Mahama ta ƙi amincewa da sharaɗin shirin na miƙa muhimman bayanai na kiwon lafiya na ƙasar.

Irin wannan damuwa game da tsaron bayanai na ta bayyana a tattaunawar Amurka da wasu ƙasashen Afirka.

Tun farkon shekarar 2026 ne dai ƙasar Zimbabwe ta nuna irin wannan damuwa yayin da a Kenya wata vkotu ta dakatar da aiwatar da yarjejeniyar na wucin gadi har zuwa lokacin da za a saurari ƙara daga wata ƙungiyar kare haƙƙin mutane masu amfani da shirin.

Sai dai kuma mai magana da yawun gwamnatin ƙasar Ghana da kuma ma’aikatar harkokin wajen ƙasar ba su amsa tambaya ta neman ƙarin haske game da lamarin ba.

Kazalika ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta ƙi ta ba da cikakken bayani game da yarjejeniyar.

“Muna ci gaba da neman hanyoyin ƙarfafa dangantakar haɗin gwiwa da ke tsakanin ƙasashenmu biyu,” in ji wani mai magana da yawun ma’aikatar.

Tsarin lafiya na duniya na gwamnatin Trump da ya fi bai wa Amurka fifiko ya zayyana wata manufa da za ta sa Amurka ta kasance a kan gaba a lafiya a duniya ta hanyar kare Amurkawa da ƙarfafa tsaron lafiyar Amurka da kuma inganaa wadata ta tsarin tallafi na ƙetare.

Tsarin na da burin rage dogaro ga tallafin ƙetare daga baya.

Bayanai na tallafin ƙetaren gwamnatin Amurka sun nuna cewa Amurka ta ba da tallafin ƙetare da ya kai dala miliyan 219 ciki har da dala miliyan 96 a kan kiwon lafiya a shekarar 2024, shekara ɗaya kafin gwamnatin Trump ta yanke tallafin ƙetare.

Yarjejeniayar da ɓangarorin biyu suka fara aiki a kai a watan Nuwamban shekarar 2025 da za ta iya samar da tallafin Amurka na dala miliyan 109 cikin shekaru biyar.

Amma ba a bayyana nauyin da ya rataya a kan Ghana a fannin kuɗi ƙarara ba a yarjejeniyar.

“Sun yi kama da yarjejeniya na yau da kullunm daga farko. Amma daga baya aka fara samun ƙarin matsi musamman a ƙarshe,” in ji rahoton.

Ranhotanni sun ce Washington ta ayyana 24 ga watan Afrilu a matsayin ranar ƙarshe ta kammala tattaunawa kan yarjejeniyar, ita kuma Ghana ta yanke shawarar cewa ba za ta yarda da abin da yarjejeniyar ke tsarawa ba.

Tuni dai Ghana ta bayyana matsayarta ga Gwamnatin Trump.