| Hausa
GABAS TA TSAKIYA
3 minti karatu
Mene ne Tehran ke gabatarwa domin kawo ƙarshen yaƙin Amurka da Isra'ila a kan Iran?
Trump ya ce ya fi son ya ci gaba da ƙawanyar sojin ruwa kan tashoshin ruwan Iran domin ƙara matsi kan Tehran.
Mene ne Tehran ke gabatarwa domin kawo ƙarshen yaƙin Amurka da Isra'ila a kan Iran?
TSOHON HOTO: Tutocin Iran suna kaɗawa Tehran a shekarar 2022. / Reuters

Iran ta gabatar da shawarar sake buɗe Mashigar Ruwan Hormuz da kuma kawo ƙarshen yaƙin yayin da take ɗaga tattaunawa game da shirin nukiliya zuwa wani lokaci na gaba, kamar yadda wani rahoton kafafan watsa labarai ya bayyana ranar Lahadi.

An gabatar da shawarwarin ne dai ga Amurka ta hanyar masu shiga tsakani ciki har da Pakistan, cikin ƙiƙi-ƙaƙa ta tattaunawa game da shirin nukiliyar Iran, in ji kafar watsa labarai ta intanet ta Axios .

Majiyoyi sun ce shirin na ƙoƙarin kauce wa rashin jituwa game da inganta yuraniyum domin cim ma yarjejeniya cikin sauri da zummar kawar da ƙawanya da kuma dawo da kaikomon hanyar ruwa, in ji kafar watsa labaran.

A ƙarƙashin shawarwarin, za a tsawaita tsagaita wuta na tsawon lokaci ko kuma a mayar da shi na dindindin , yayin da tattaunawa game da nukiliya zai fara ne kawai bayan an sake buɗe mashigin kuma an kawar da ƙuntatawa.

Wani jami’in Amurka da kuma wasu majiyoyi da suke sane da tattaunawar sun ce fadar White House ta karɓi shawarwarin amma ba nuna ko za ta bi su ba.

Ana tsammanin Shugaba Donald Trump ya yi wata ganawa ta yadda abubuwa ke tafiya ranar Litinin da manyan jami’an tsaron ƙasa domin tattauna cijewar lamarin da kuma matakan da za a iya ɗaukawa nan gaba.

Trump ya ce shi ya si son ya ci gaba da ƙawanyar ta sojin ruwa kan tashoshin jiragen ruwan Iran domin ƙara matsi kan Tehran.

“A lokacin da kake da mai mai yawa, idan aka rufe wannan wannan layin, layin zai fashe daga cikin,” a cewarsa, yana mai ƙarawa da cewa Iran za ta iya kasancewa tana da “kimanin kwanaki uku” kafin su fuskanci matsi daga cikin gida.

An zafafa matakan diflomasiyya cikin ƙarshen mako , inda ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya tattauna a Islamabad, a Pakistan, da Muscat, a Oman, inda ya mayar da hankali kan mashigin ruwan.

Ya isa Saint Petersburg, a Rasha, da sanyin safiyar ranar Litinin domin tattaunawa da shugaban Rasha Vladimir Putin da sauran manyan jami’ai.

“Waɗannan tattaunawa na didlomasiyya masu muhimmanci ne. Amurka ce ke da bakin zaren,” in ji mai magana da yawun fadar White House Olivia Wales.

Iran da Amurka sun tattauna a Islamabad tsakanin ranar 11 zuwa 12 a watan Afrilu, amma sun gaza cim ma wata matsaya ta kawo ƙarshen rikicin.

Tattaunawar na ta zo ne bayan Pakistan ta taimaka wajen samar da tsagaita wuta na mako biyu ranar 8 ga watan Afrilu, wadda daga baya Trump ya tsawaita ta.

Duk da cewa an fara ƙoƙarin wani zagaye na tattaunawa, wasu daga cikin batutuwan da suka ba jan hankali zun haɗa da Mashigar Ruwan Hormuz da ƙawayanyar da Amurka ta yi wa tashoshin jiragen ruwan Iran da kuma ‘yancin Iran na inganta yuraniyum.