Shugaba Donald Trump bai yarda da tayin Iran na sake buɗe Mashigar ruwan Hormuz da kuma kawo ƙarshen yaƙin Amurka da Isra’ila a kan Iran ba, in ji wani rahoto.
An yi wa Trump bayani game da shirin Tehran, wanda ya kuma haɗa da kawo ƙarshen ƙawanyar Amurka kan muhimman hanyoyin ruwa, a lokacin wani zaman ɗakin bibiyar abubuwan da ke wakana a fagen daga a Fadar White House ranar Litinin, kamar yadda jaridar The New York Times ta ruwaito, inda ta ambato majiyoyin da ba a bayyana sunayensu ba waɗanda aka bai wa labarin tattaunawar.
Shawarar ba ta shafi abin da zai faru da shirin nukiliyar Iran ba, kamar yadda jami’an Amurka da na Iran suka shaida wa Times.
A baya dai Iran ta yi watsi da buƙatun Amurka da ke neman ta dakatar da sarrafa yuraniyom, tana mai cewa tana da ‘yancin yin hakan a ƙarƙashin dokar ƙasa da ƙasa, kuma kawo yanzu ta ƙi ta miƙa yuraniyom ɗin da ta riga ta sarrafa.
Babu tabbacin abin da Trump bai yarda da shi ba, amma ya daɗe da dagewa kan buƙatun biyu na nukiliya.
“Amurka ba za ta yi yarjejeniya ta kafafen watsa labarai ba — mun bayyana abubuwan da ba za mu lamunta ba kuma shugaban ƙasa zai ƙulla yarjejeniyar da ke da kyau ga Amurkawa da duniya ne kawai ,” kamar yadda mai magana da yawun Fadar White House Olivia Wales ta shaida wa Times.
Koma-baya ga tattaunawar zaman lafiya?
Axios ta ba da rahoto game da shawarwarin ranar Lahadi, jim kaɗan bayan ta ce ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya miƙa sharwarwarin ga masu shiga tsakani na Pakistan.
A ƙarƙashin shawarwarin, za a tsawaita tsagaita wuta na lokaci mai tsawo ko kuma na dindindin, yayin da tattaunawar nukiliay za ta fara ne kawai bayan an sake buɗe mashigar ruwan Hormuz, in ji Axios.
A makon da ya gabata Trump ya yi watsi da da wasu shawarwari daga Iran, kuma aka soke tattaunawa da aka shirya yi a birnin Islamabad na Pakistan a ƙarshen mako.
Jami’an Amurka sun shaida wa The New York Times cewa Iran ba ta bai wa masu tattaunawa izinin rage komai ba dangane da shirin nukiliyarta, lamarin da ya janyo babban koma-baya ga tattaunawar zaman lafiyar.
Muhawarar da ake yi a cikin gwamnatin Trump a halin yanzu ita ce wahalar tattalin arziki nawa ne Iran za ta iya jurewa sakamakon ƙawanyar da Amurka ta yi wa mashigar ruwan Hormuz, da kuma tasirin da take da shi kan tattalin arzikin ƙasar.
Man da ake fitarwa yana fin ƙarfin rumbunan ajiyar mai cikin sauri kuma ba za a iya rufe rijiyoyin mai ba.
Za a iya samun ɓarna mai yawa idan ba a rufe su ba, kuma wasu daga cikin gwamnatin suna cewa Iran za ta shiga yarjejeniya maimakon ta tafka asarar, kamar yadda Times ta ruwaito.
















