Masana kimiyya da masu bincike a Kenya sun dukufa wajen yin nazarin yadda za su samar da shanun da aka 'Sauya Kwayoyin Halittarsu'.
A lokaci guda, wadannan shanu da aka Sauya wa Kwayoyin Halitta za su samar da madara da nama sama da yadda aka saba gani.
Masu binciken sun yi ikirarin cewa wannan sabon yunkuri na iya zama mafita ga kalublen da makiyaya dabbobi ke fuskanta.
Sun kuma ce kokarin na iya taimaka wa wajen rage fitar da gurbatacciyar iskar gas tare da sanya noma da kiwo zama masu inganta muhalli.
Masu binciken na Kenya za su hada kai da abokan aiki na cikin guda da na waje.
Sai dai kuma, fasahar Sauya Kwayoyin Halitta na ci gaba da janyo babbar muhawara saboda damuwa kan tsaro, dokoki da akidun jama’a.
Sakamakon haka, kokarin na yawan fuskantar adawa mai karfi daga masu ruwa da taki da dama a bangaren ayyukan noma, kare muhalli, da ma bangaren kiwon lafiya.
An kaddamar da shirin a wajen zama kan Sauya Kwayoyin Halittar abubuwa a wajen Babban Taron Kungiyar likitocin Dabbobi ta Kenya karo na 60 a gundumar Kwale da ke gabar tekun Kenya.
Duk da batun na kan gabar bincike, da yawan mutane sun fara tamayar ko wannan zai zama makomar kiwon dabbobi a Kenya?















