Chadi ta ayyana zaman makoki na ƙasa na kwanaki uku bayan wani sabon harin ‘yanta’addan Boko Haram ranar Laraba ya kashe janar-janar biyu a yankin Tafkin Chadi.
Da yammacin ranar Litinin, wani hari kan sansanin soji na Barka Tolorom a gaɓar Tafkin Chadi da ke ƙasar ya yi sanadin mutuwar aƙalla sojoji 24 inda saura suka jikkata, in ji wata majiyar soji.
Ranar Laraba da rana, jiragen ruwa na tsaro da ke sintiri a yankin tsibirin Tafkin Chadi "sun faɗa a wani kwanton-ɓauna na Boko Haram," kamar yadda wani hafsa sojin ƙasar ya shaida wa kamfanin dillancin labaran AFP, yana mai ƙarawa da cewa an kashe janar-janar biyu a harin.
Gwamnatin ƙasar ta ayyana zaman makokin na ƙasa a wata sanarwa "daga ranar Laraba, 6 ga watan Mayu zuwa Asabar 9 ga watan Mayu a tsakar dare...domin tunawa da shahidan da suka rasa rayukansu a fagen yaƙi na martaba yayin hare-haren ƙungiyoyin ta’addanci da suka faru ranakun 4 da 6 ga watan Mayu".
An haramta bukukuwa
Yayin wannan lokacin, tutoci za su kasance ƙasa-ƙasa kuma an haramta dukkan bukukuwa a faɗin ƙasar, in ji ta.
"Za mu ci gaba da da yaƙi cikin jajircewa har sai mun kawar da wannan barazanar gaba ɗaya," kamar yadda Shugaban ƙasar Chadi Mahamat Idriss Deby Itno ya bayyana bayan harin na ranar Litinin.
Sojojin Chadi suna yawan fuskantar hare-haren Boko Haram a yankin Tafkin Chadi, wani babban wuri mai ruwa da fadamu mai tsibirai da ke tsakanin Nijeriya da Kamaru da Nijar da Chadi.
Tun shekarar 2009, ya kasance wani wuri da ‘yanta’adda ke da ƙarfi da yake kare mayaƙan Boko Haram da abokiyar hamayyarta, ISWAP.
Ƙaruwar hare-hare
An samu ƙarin hare-haren ɓangarorin Boko Haram cikin ‘yan watannin nan, ciki har da garkuwa da mutane da kuma hare-hare kan sansanonin jami’an tsaro.
A watan Oktoban shekarar 2024, wani mummunan harin Boko Haram kan wani sansanin soji a tafkin Chadi ya kashe sojoji Chadi 40.
A matsayin martani, Shugaba Deby ya ƙaddamar da aiki na musamman mai suna ‘Operation Haskanite’ domin "kassara ikon Boko Haram na iya haddasa rauni."
Rundunar sojin Chadi ta kammala harin ramuwar gayyarta a watan Fabrairun shekarar 2025, tana mai tabbatar da cewa ƙungiyar ta ‘yan ta’adda ba ta da “wani wurin zaman a ƙasar Chadi."







