Rundunar sojin Mali da abokan ƙawancenta sojojin haya na Rasha sun fice daga wani muhimmin sansanin soja da ke arewacin ƙasar inda suka bar wa ’yan tawaye, yayin da ’yan tawayen Abzinawa masu neman ɓallewa da sauran mayaka suka haɗa kai don kifar da gwamnatin sojan ƙasar.
Ƙasar ta yammacin Afirka tana fuskantar mawuyacin hali na tsaro biyo bayan munanan hare-hare da aka kai a ƙarshen makon da ya gabata a sansanonin soji daban-daban, waɗanda ƙungiyoyin FLA (Azawad Liberation Front) da JNIM (Group for the Support of Islam and Muslims) suka ƙaddamar.
Yayin hare-haren, ’yan tawayen sun kashe ministan tsaron Mali sannan suka ƙwace muhimmin garin Kidal da ke arewa. A ranar Juma’a, dakarun da ke babban sansanin Tessalit da ke kusa da kan iyakar Aljeriya sun tsere daga sansanin sannan suka gudu zuwa kudu, kamar yadda wani jami’in FLA ya shaida wa kamfanin AFP.
Wannan ficewa na zuwa ne kwana guda bayan da ƙungiyar JNIM mai alaƙa da Al Qaeda ta fara killace hanyoyin da ke kaiwa babban birnin ƙasar, Bamako. Mutanen da ke cikin birnin ne kawai aka bai wa damar fita.
Wata majiyar tsaro a Gao ta shaida wa AFP cewa ba a yi wani artabu ba a Tessalit, domin sojojin ƙasar sun riga sun fice kafin maharan su shiga. Haka kuma, wani jami’i na yankin ya tabbatar da cewa dakarun Rasha sun gudu sun bar wuraren da suke.
Sansanin na Tessalit yana da matuƙar muhimmanci saboda yanayin wurin da yake da kuma filin jirgin sama mai kyau da zai iya ɗaukar manyan jiragen yaƙi da masu saukar ungulu.
Kazamin fada
Waɗannan hare-hare na haɗin gwiwa da aka kai a ƙarshen mako sun kasance mafiya muni da aka gani a Mali a kusan shekaru 15. Ƙazamin faɗan da aka yi a wurare daban-daban, ciki har da kusa da Bamako, ya yi sanadiyar mutuwar akalla mutane 23, ciki har da Ministan Tsaro Sadio Camara.
An gudanar da taron karrama marigayi ministan mai shekaru 47 a ranar Alhamis, wanda ya mutu sakamakon harin bam da aka ɗana a mota a gidansa da ke Kati, wani garin sojoji kusa da Bamako.
Asusun Kula da Ƙananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya bayyana a ranar Juma’a cewa fararen hula da yara sun mutu, sannan wasu sun ji rauni yayin hare-haren. An kuma bayar da rahoton wani harin a wata cibiyar lafiya a Gao, yayin da aka mamaye wata makaranta a yankin Mopti.
Ofishin mai gabatar da ƙara na soja a Bamako ya yi zargin cewa wasu sojoji da tsofaffin sojoji sun taimaka wajen tsarawa tare da aiwatar da waɗannan hare-hare. Haka kuma an zargi ɗan siyasar hamayya Oumar Mariko da hannu a ciki.
A shekarun baya bayan nan, ƙasar Mali, tare da maƙwabtanta Burkina Faso da Nijar, sun yanke hulɗa da tsohuwar uwar gijiyarsu, Faransa. Waɗannan ƙasashe uku sun haɗa kai inda suka kafa ƙungiyar Alliance of Sahel States (AES), wadda ta samar da haɗakar dakarun soja kusan 15,000.
Gwamnatin Nijar ta bayyana da maraicen ranar Alhamis cewa ƙasashe ukun sun “gudanar da munanan hare-hare ta sama” biyo bayan hare-haren da aka kai a Mali ranar Asabar da ta gabata.
Yayin da wancan harin ya kasance babban sauyi a yaƙin da JNIM ke yi da gwamnatin sojan Mali, ba shi ne kaɗai harin da ’yan tawayen suka ƙaddamar ba a baya bayan nan.
A ƙarshen shekarar da ta gabata, ƙungiyar JNIM ta yi ƙoƙarin durƙusar da tattalin arziƙin Mali ta hanyar sanya takunkumin katse hanyoyin samar da man fetur da dizil da ake shigo da su daga ƙasashen waje ta hanyar amfani da manyan motoci, musamman daga ƙasashen Ivory Coast da Senegal.
AFIRKA
4 minti karatu
’Yan tawaye sun ƙwace muhimmin sansani daga sojojin Mali da sojojin haya na Rasha - rahotanni
’Yan tawaye ƙarƙashin jagorancin Abzinawa da sauran 'yan tawaye sun ƙwace babban sansanin “super-camp” na Tessalit da ke kusa da kan iyakar Aljeriya, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito.
Rumbun Labarai














