Gwamnatin ƙasar Uganda ta kama ‘yan Nijeriya 62 kan zargin gudanar da wani coci ba bisa ƙa’ida ba, tare da zama da aiki a ƙasar ba tare da sahihan takardun izinin aiki ba.
A wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X ranar Laraba, hukumar shige da fice ta ƙasar (NCIC), ta ce kamen ya biyo bayan bayanan sirri da ta samu ne bayan ta gano cewa mutanen suna aiki a ƙasar ba tare da takardun izinin da ake buƙata ba.
“Bayan samun bayanan sirrin, jami’anmu masu tabbatar da doka sun kama ‘yan Nijeriya 62 da ake aiki ba bisa ƙa’ida ba a Adjumani (ba tare da takardun izinin aiki ba),” in ji sanarwar.
“Mutanen, waɗada yawancinsu aka samu suna gudanar da wani coci da sauran abubuwa, a halin yanzu ana tattara bayanai daga gare su domin gurfanar da su a kotu a ƙarƙashin hukumar shige da ficen Uganda.”
Simon Peter Mundeyi, wani mai magana da yawun ma’aikatar tsaron cikin gidan ƙasar, ya ce sau da yawa ‘yan Nijeriya suna fitowa ne a matsayin masu wa’azin yaɗa bishara kuma suna aikata wasu ayyuka da suka saɓa wa doka.
Ya ƙara da cewa a halin yanzu ana riƙe da su ne a wani wuri na ma’aikatar da ke Namanve, inda ake bincike a kansu wanda zai iya sa wa a tasa ƙeyarsu ko a ci tararsu ko kuma a hana su shiga ƙasar har abada.
“Yawanci suna fitowa ne a matsayin masu wa’azin yaɗa bishara yayin da suke aikata wasu ayyuka ba bisa ƙa’ida ba. Yayin da muke aiki bisa bayanan sirri, mun shiga kuma mun kama su,” in ji Mundeyi.
Mundeyi ya ce bincike wucin-gadi ya nuna bayanai masu karo da juna daga bakin waɗanda ake zargin, yana mai ƙarawa da cewa wasu sun yi iƙirarin cewa da yaudara aka kai su Uganda da takardun ayyuka na bogi, yayin da ake zargin sauran da kasancewa masu damfara ta intanet da laifuka masu alaƙa da shi.







