Tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani na Nijeriya, Isa Ali Ibrahim Pantami, ya sanar da janyewarsa daga zaben fidda gwani na jam’iyyar APC domin takarar gwamnan Jihar Gombe, inda ya danganta matakin da zargin take Dokar Zabe ta 2026 da kuma rashin gaskiya a tsarin gudanar da zaben cikin gida na jam’iyyar.
A cikin wata sanarwa da Barrista Ibrahim M. Attahir ya fitar a ranar Talata, Farfesa Pantami ya ce ya dauki matakin ne bayan tuntubar masu ruwa da tsaki da kuma yin nazari kan abubuwan da suka faru dangane da zaben fidda gwani na APC a jihar.
Pantami ya bayyana cewa duk da ya bi dukkan ka’idojin jam’iyyar bayan amsa kiraye-kirayen matasa, mata da shugabannin al’umma da suka bukace shi da ya tsaya takara, ana ci gaba da hana shi samun muhimman bayanan da suka dace domin gudanar da sahihin zabe.
Sanarwar ta ce lauyoyinsa sun aika wasiku zuwa shugabannin APC suna neman karin haske kan hanyoyin gudanar da zabe, tantance wakilai, cibiyoyin tattara sakamako da sauran muhimman bayanai, amma ba a mayar musu da martani ba.
Tsohon ministan ya kuma nuna damuwa kan yadda aka gudanar da zabukan fidda gwani na ‘yan majalisar dokoki da aka yi a ranakun 16 da 18 ga watan Mayu, inda ya ce an ware mambobin jam’iyyar na kasa daga tsarin zaben, duk da cewa an sanar da sakamako.
Pantami ya ce karfinsa a siyasa ya fi fitowa ne daga goyon bayan matasa da mata a matakin kasa, yana mai cewa irin wadannan kura-kurai sun saba wa tsarin dimokuradiyya da tanadin Dokar Zabe ta 2026.
Ya kuma bayyana cewa shi ne kadai daga cikin masu neman takarar gwamna na APC da ya aika wakili wajen taron yarjejeniyar zaman lafiya da Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta shirya a Gombe ranar 14 ga Mayu, inda wakilinsa shi kadai ya sanya hannu kan yarjejeniyar.
Yayin da yake sanar da janyewarsa daga zaben fidda gwani na APC da aka shirya yi ranar 21 ga Mayu, Pantami ya bayyana matakin a matsayin zanga-zangar lumana domin kare dimokuradiyya, bin doka da gudanar da sahihin zabe.
Sanarwar ta kuma yaba wa magoya bayansa, musamman matasa da suka tara kudade domin sayen fom dinsa na nuna sha’awa da tsayawa takara, inda gudummawar ta kai daga Naira dubu biyar zuwa miliyan hudu.
Pantami ya bukaci dukkan magoya bayan kungiyar Pantamiyya da su kasance masu bin doka da oda tare da kiyaye zaman lafiya, yana mai tabbatar da cewa kungiyar za ta sanar da matakinta na gaba da shirinta a siyasance nan gaba kadan.
Ya jaddada kudirin kungiyar na ci gaba da fafutukar samar da shugabanci nagari a Jihar Gombe da Najeriya baki daya ta hanyar lumana da bin tsarin dimokuradiyya.











