| Hausa
GABAS TA TSAKIYA
3 minti karatu
Iran ta bayyana cikakkun bayanai na shawarwari 14 ga Amurka da nufin kawo ƙarshen yaƙi
Haka kuma shawarwarin sun tabbatar da “dage dukkan takunkumai da kuma kudurorin Majalisar Tsaro ta Majalisar Ɗinkin Duniya, da janye sojojin Amurka daga yankunan da ke kusa da Jamhuriyar Musulunci ta Iran,” in ji shi.
Iran ta bayyana cikakkun bayanai na shawarwari 14 ga Amurka da nufin kawo ƙarshen yaƙi
Iran ta bayyana cikakkun bayanai na shawarwari 14 ga Amurka da nufin kawo ƙarshen yaƙi / AP

A ranar Talata ne Iran ta bayyana cikakkun bayanai na sabuwar shawararta da ta miƙa wa Amurka domin kawo ƙarshen yaƙin da Washington da Isra’ila suka ƙaddamar kan Tehran a watan Fabrairu.

An bayyana cikakkun bayanan ne daga mataimakin ministan harkokin wajen Iran, Kazem Gharibabadi, yayin wata ganawa da mambobin kwamitin tsaro na ƙasa da manufofin waje na majalisar dokoki, inda ya gabatar da cikakken rahoto kan sabbin ci gaba a harkokin diflomasiyya tsakanin Iran da Amurka.

Gharibabadi ya ce shawarwarin Tehran sun jaddada “haƙƙin ƙasar na tace sinadarin uranium da gudanar da ayyukan nukiliya na zaman lafiya,” kamar yadda kamfanin dillancin labarai na hukuma IRNA ya ruwaito.

Shawarwarin kuma sun haɗa da “kawo ƙarshen rikice-rikice a dukkan fannoni, ciki har da Lebanon; ɗage takunkumi kan sojojin ruwan Amurka; sakin kadarorin Iran da aka ƙwace; da kuma biyan diyya daga Amurka kan barnar da aka yi yayin yaƙin na baya-bayan nan domin taimakawa ayyukan sake gina ƙasar.”

Haka kuma shawarwarin sun tabbatar da “dage dukkan takunkumai da kuma kudurorin Majalisar Tsaro ta Majalisar Ɗinkin Duniya, da janye sojojin Amurka daga yankunan da ke kusa da Jamhuriyar Musulunci ta Iran,” in ji shi.

A ranar 10 ga Mayu, Iran ta mika martaninta ga shawarar Amurka da nufin kawo ƙarshen yaƙin ta hanyar Pakistan, amma Shugaba Donald Trump ya bayyana shawarar Iran a matsayin “wacce ba za a amince da ita ba kwata-kwata.”

Kafofin yada labarai na Iran sun ruwaito a ranar Litinin cewa Iran ta sake gabatar da sabuwar shawarwari mai matakai 14 ga bangaren Amurka ta hannun masu shiga tsakani daga Pakistan.

A ranar Asabar, Trump ya sake yin barazanar ƙarin farmakin soja kan Iran, inda ya wallafa hoto a dandalinsa na Truth Social wanda ke nuna jiragen ruwa na yaƙi masu tutar Amurka, ciki har da wani jirgi da ke ɗauke da tutar Iran, tare da rubutun “IT WAS CALM BEFORE THE STORM.”

A yammacin Litinin kuma, Trump ya sanar cewa ya dakatar da wani harin soja da aka shirya kai wa Iran a ranar Talata, bisa buƙatar Saudiyya, Qatar da Hadaddiyar Daular Larabawa.

Ya kuma ƙara da cewa ya umarci Ma’aikatar Tsaro “ta kasance cikin shiri don kai cikakken babban hari kan Iran cikin gaggawa, idan har ba a cim ma yarjejeniyar da ta dace ba.”

Bayan tattaunawar da ta tsaya cak da Pakistan ke shiga tsakani, Amurka ta kakaba toshewar tashoshin jiragen ruwan Iran tun daga ranar 13 ga Afrilu, ciki har da waɗanda ke kan mashigar ruwa mai muhimmanci ta Hormuz.

Iran ta mayar da martani ta hanyar rufe mashigar, tare da tilasta jiragen ruwa su rika neman izini daga Tehran kafin wucewa, a yayin da ake fargabar cewa tsagaita wuta mai rauni da ake da ita tun 8 ga Afrilu na iya rushewa idan ba a cim ma yarjejeniya ba ta kawo ƙarshen yaƙin.

Rumbun Labarai
Trump ya sanar da cim ma yarjejeniyar Iran mai tarihi, ya yi alƙawarin buɗe Mashigar Hormuz nan-take
Yarjejeniyar Amurka da Iran ta ƙunshi sake buɗe Hormuz, taƙaita aikin nukiliya: babban jami'i a Iran
An gano wani dutse mai ɗauke da rubutun sunan Khalifa Umar ibn Khattab a Madina
Iran ta kai hare-hare manyan cibiyoyin sojin Amurka 18 a Kuwait da Bahrain yayin da hankula ke tashi
Amurka ta kai hare-hare da dama ta sama Iran yayin da hankula suka tashi kan sake ɓarkewar yaƙi
Helikwaftan sojin Amurka ya faɗi kusa da Mashigar Hormuz; matuƙansa suna 'lafiya', in ji Trump
Ƙungiyar Houthi ta yi barazanar haramta wa Isra'ila jigilar kayayyaki a Bahar Rum gaba ɗaya
Isra'ila ta ƙaddamar da hare-hare a faɗin Iran yayin da yaƙin Gabas Ta Tsakiya ya sake ɓarkewa
Iraniyawa sun nuna juriya da ƙalubale irin na lokacin yaƙi a wani gagarumin gangami a Tehran
Fashe-fashe sun girgiza tsibirin Qeshm na Iran yayin da Kuwait ta tare jerin makamai masu linzami
Iran ta ce ta kai hari kan wani jirgi mai alaƙa da Amurka da Isra'ila bayan hari kan wani jirginta
Iran ta dakatar da tattaunawa da Amurka saboda hare-haren Isra'ila a Lebanon: rahoto
Iran ta kai hari sansanin sojin Amurka a Kuwait bayan hari kan benen sadarwar Hormozgan
Masar ta yi kira ga kwamitin tsaro na MƊD ta dakatar da faɗaɗa [harin] da Isra'ila ke yi a Lebanon
Iran ta ci gaba da aikin samar da gas a wurarenta uku na South Pars da ke cikin teku
Netanyahu ya kira taron gaggawa bayan Hezbollah ta kai hari na ban mamaki ga sojin Isra'ila
Zaman jiragen sojojin Amurka ya janyo wa filin jirgin saman Ben Gurion na Israila asarar $248M
Dakarun Juyin-Juya-Hali na Iran sun ce sun kai hari sansanin Amurka na sama a Kuwait
Amurka ta kai sabbin hare-hare a wuraren soji a kudancin Iran — rahoto
Rundunar sojin Isra'ila ta yi ikirarin kashe shugaban rundunar sojin Hamas a wani babban hari a Gaza