Wani babban jami'in Iran ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa daftarin yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Iran da Amurka ya ƙunshi batutuwa daga shirin nukiliyar Tehran zuwa sake buɗe Mashigar Hormuz da kuma sassaucin Amurka kan takunkumin man fetur.
Jami'in ya ce za a tattauna yarjejeniya ta ƙarshe cikin kwanaki 60 idan dukkan ɓangarorin sun amince da wannan daftarin.
Daftarin ya ƙunsa abubuwan kamar:
Mashigar Hormuz
Iran za ta buɗe Mashigar Hormuz nan take ga dukkan jiragen kasuwanci, yayin da Amurka za ta janye sojin ruwanta da ta yi amfani da su ta toshe tashoshin ruwan Iran.
Matakan kuɗi
Amurka za ta yarda ba za ta ƙara ƙaƙaba sabbin takunkumai kan Iran ba har sai an cim ma yarjejeniya ta ƙarshe.
Washington za ta sassauta takunkumin mai kan Iran na wani lokaci da aka ƙayyade, wanda zai ba Tehran damar sayar da mai da samun kuɗaɗen shiga.
Amurka za ta kuma yarda a saki dala biliyan 25 na kadarorin Iran da aka ƙwace, ciki har kuɗi lakadan da aka yi taransfa ɗinsu kai tsaye, haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen yanki da samar da hanyoyin bashi na banki.
Batutuwa na nukiliya
Tehran za ta amince ba za ta ƙera ko samo makaman nukiliya ba.
Iran za ta ci gaba da kasancewa a matakin da take a yanzu ta fuskar nukiliyarta har sai an cim ma yarjejeniya ta ƙarshe, ciki har da rashin haɓaka uranium ko faɗaɗa cibiyoyin nukiliya.
Amurka za ta amince cewa Tehran za ta surka tarin ingantaccen uranium ɗinta a cikin ƙasar, inda za a tattauna yadda za a aiwatar da hakan cikin kwanaki 60.





.jpeg?width=512&format=webp&quality=80)








