| Hausa
GABAS TA TSAKIYA
2 minti karatu
Zaman jiragen sojojin Amurka ya janyo wa filin jirgin saman Ben Gurion na Israila asarar $248M
Kaso ɗaya cikin uku na filin jirgin ne kawai ke aiki yanzu, saboda gomman jirage Amurka masu dakon mai sun mamaye filin jirgin.
Zaman jiragen sojojin Amurka ya janyo wa filin jirgin saman Ben Gurion na Israila asarar $248M
Jiragen saman dakon mai na rundunar sojin saman Amurka suna fake a filin jirgin saman kasa da kasa na Ben Gurion da ke Lod, kusa da Tel Aviv. / Reuters

Zaman jiragen rundunar sojin Amurka a Filin Jirgin Ben Gurion na Isra’ila ya janyo wa hukumar filayen jirgin kasar asarar shekel miliyan 700 (kimanin dalar Amurka miliyan 248) a watanni biyu da suka gabata, in ji jami’an Isra’ila, wadanda suka yi gargaɗin cewa adadin na iya tashi zuwa biliyoyi idan lamarin ya ci gaba.

Sharon Kedmi, Darakta Janar na Hukumar Filayen Jirgin Sama ta Isra’ila, ya faɗa a ranar Alhamis cewa, a halin yanzu kashi ɗaya cikin uku na Filin Jirgin Ben Gurion ne kawai yake aiki, saboda kasancewar jiragen sojin Amurka masu dakon mai sun cika shi, a cewar bayanan da gidan talabijin na gwamnati KAN ya ruwaito.

'Muna amfani ne kawai da ƙashi ɗaya cikin uku na filin jirgin,' in ji Kedmi, sannan ya ƙara da cewa an takaita kimanin kashi 70 cikin 100 na ayyukan filin saboda rashin waje da kuma kayan ayyukan sojin Amurka da suka mamaye shi.

'Mun kai iyakar abin da za mu iya,' in ji shi, yana gargadin cewa za a sanar da karin soke tafiye-tafiye cikin 'yan kwanaki masu zuwa.

Kedmi ya yi gargaɗin cewa asarar na iya kaiwa biliyoyin shekels idan yanayin ya ci gaba.

'Filin jirgin soja da ake ayyukan fararen hula kadan'

Ya ƙara da cewa hukumomin filayen jirgin sama sun sa rai fasinjoji miliyan 18 za su bi ta Ben Gurion a wannan shekara, amma ƙiyasin yanzu yana nuna adadin na iya ƙasa ya wuce miliyan 15.

Ya ce kamfanonin jiragen sama na ƙasashen waje ma ba za su yiwuwar dawo da ayyukansu nan ba da jimawa ba, yayin da har zuwa fasinjoji miliyan 3 za su iya fuskantar cikas da soke tafiye-tafiye.

A halin yanzu, jiragen dakon mai da yawa na sojin Amurka suna ajiye a Filin Jirgin Ben Gurion.

A farkon wannan watan, kafofin watsa labarai na Isra’ila sun ruwaito Shugaban Hukumar Kula da Jiragen Sama, Shmuel Zakay, yana cewa jiragen sojin Amurka a Ben Gurion suna raunana tashi da saukar fararen hula, suna jinkirta dawowar kamfanonin jiragen waje kuma suna ɗaga farashin tikiti.

An kuma ambaci Zakay yana gaya wa Ministar Sufuri ta Isra’ila, Miri Regev, cewa Ben Gurion 'ya zama filin jirgin soja tare da ayyukan fararen hula da suka takaita,' yana gargadin cewa lamarin na cutar da kamfanonin jiragen sama na cikin gida.

Rumbun Labarai
Trump ya sanar da cim ma yarjejeniyar Iran mai tarihi, ya yi alƙawarin buɗe Mashigar Hormuz nan-take
Yarjejeniyar Amurka da Iran ta ƙunshi sake buɗe Hormuz, taƙaita aikin nukiliya: babban jami'i a Iran
An gano wani dutse mai ɗauke da rubutun sunan Khalifa Umar ibn Khattab a Madina
Iran ta kai hare-hare manyan cibiyoyin sojin Amurka 18 a Kuwait da Bahrain yayin da hankula ke tashi
Amurka ta kai hare-hare da dama ta sama Iran yayin da hankula suka tashi kan sake ɓarkewar yaƙi
Helikwaftan sojin Amurka ya faɗi kusa da Mashigar Hormuz; matuƙansa suna 'lafiya', in ji Trump
Ƙungiyar Houthi ta yi barazanar haramta wa Isra'ila jigilar kayayyaki a Bahar Rum gaba ɗaya
Isra'ila ta ƙaddamar da hare-hare a faɗin Iran yayin da yaƙin Gabas Ta Tsakiya ya sake ɓarkewa
Iraniyawa sun nuna juriya da ƙalubale irin na lokacin yaƙi a wani gagarumin gangami a Tehran
Fashe-fashe sun girgiza tsibirin Qeshm na Iran yayin da Kuwait ta tare jerin makamai masu linzami
Iran ta ce ta kai hari kan wani jirgi mai alaƙa da Amurka da Isra'ila bayan hari kan wani jirginta
Iran ta dakatar da tattaunawa da Amurka saboda hare-haren Isra'ila a Lebanon: rahoto
Iran ta kai hari sansanin sojin Amurka a Kuwait bayan hari kan benen sadarwar Hormozgan
Masar ta yi kira ga kwamitin tsaro na MƊD ta dakatar da faɗaɗa [harin] da Isra'ila ke yi a Lebanon
Iran ta ci gaba da aikin samar da gas a wurarenta uku na South Pars da ke cikin teku
Netanyahu ya kira taron gaggawa bayan Hezbollah ta kai hari na ban mamaki ga sojin Isra'ila
Dakarun Juyin-Juya-Hali na Iran sun ce sun kai hari sansanin Amurka na sama a Kuwait
Amurka ta kai sabbin hare-hare a wuraren soji a kudancin Iran — rahoto
Rundunar sojin Isra'ila ta yi ikirarin kashe shugaban rundunar sojin Hamas a wani babban hari a Gaza
Musulmai sun yi sallar idin Babbar Sallah a Masallacin Ƙudus a Gabashin Birnin Ƙudus da aka mamaye