Harabar Masallacin Al-Aqsa a Gabashin Ƙudus da aka mamaye, ya cika da masu yin Sallar idi Babba a ranar Laraba, ranar farko ta hutun kwanaki hudu na Babbar Sallah.
A wannan rana Musulmai kan yi layya da dabbobi don tunawa da hadayar Annabi Ibrahim, sannan ana raba naman dabbobin ga mabuƙata a cikin al'umma.
Hutun Babbar Sallah na wannan shekara, daya daga cikin manyan bukukuwa a kalandar Musulunci, ya zo ne a yayin da ake ci gaba da saɓa alƙawarin tsagaita wuta da Isra'ila ke yi, wadda ta fara aiki tun Oktoba 2025.
A ranakun da suka gabata kafin Sallah, sojojin Isra'ila sun kai samame garuruwan Falasɗinawa a kudancin Gaɓar Yamma da Kogin Jordan da ake mamaye, inda suka tilasta wa 'yankasuwa rufe shagunansu tare da dukan wasu mazauna, in ji shaidu da kuma kafar yaɗa labaran gwamnatin Falasɗinawa.
An kai waɗannan samame a lokutan da ake tsaka da sayayya, yayin da cibiyoyin kasuwanci suka cika da jama’a suna shirin bukukuwan Babbar Sallah, bayan gwamnatin Falasɗinu ta bayar da wani ɓangare na albashin ma'aikatan gwamnati.
Babban samame ya fi mayar da hankali kan Dura, kudu da Al-Khalil a Hebron, inda shaidu suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu cewa motocin sojin Isra'ila sun shiga tsakiyar garin, yayin da jama'a ke tsaka da hada-hada, sannan sojojin suka bazu a tituna, suka ringa harba hayaƙi mai sa hawaye, kuma suka tilasta wa masu shaguna rufe kantunansu.
Farmakin ya zo ne yayin da rundunar sojin Isra'ila ke ci gaba da ƙara matsa lamaba a Gaɓar Yammacin Kogin Jordan da ake mamaye, ciki har da kashe-kashe, da tsare mutane da samame a birane da ƙauyuka da binciken gidaje da lalata dukiyoyi, tun daga lokacin da Isra’ila ta fara kisan ƙare-dangi a Gaza a Oktoban 2023.












