| Hausa
GABAS TA TSAKIYA
2 minti karatu
Trump ya sanar da cim ma yarjejeniyar Iran mai tarihi, ya yi alƙawarin buɗe Mashigar Hormuz nan-take
"Na ba da cikakkken izinin buɗe Mashigar Hormuz, haka kuma a lokaci guda, na ba da izinin janye killacewar da jiragen ruwa yaƙin Amurka suka yi nan-take," a cewar shugaban Amurka a ranar Lahadi.
Trump ya sanar da cim ma yarjejeniyar Iran mai tarihi, ya yi alƙawarin buɗe Mashigar Hormuz nan-take
Trump ya wallafa a shafinsa na Truth Social yana tabbatar da cewa yarjejeniyar tsagaita bude wuta da Iran “yanzu ta kammala”. (Hoto: FILE) / Reuters

Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da cewa an kammala yarjejeniya da Iran kuma ya ce ya ba da izinin sake buɗe Mashigar Hormuz da kuma janye killacewar rundunar sojan ruwa ta Amurka.

"Yarjejeniyar da aka yi cim mam da Jamhuriyar Musulunci ta Iran yanzu ta kammala. Ina taya kowa murna!," Trump ya bayyana a wani rubutu a dandalinsa na Truth Social.

"Don haka na ba da cikakken izinin buɗe Mashigar Hormuz ba tare da cajin kuɗi ba, kuma a lokaci guda ina ba da izinin cire katangar rundunar sojan ruwa ta Amurka nan-take," kamar yadda ya ƙara bayyanawa.

Trump ya kuma nuna cewa zirga-zirgar ruwa da jigilar makamashi za su dawo ta wannan muhimmiyar mashiga, inda ya rubuta: "Jiragen ruwa na duniya, ku kunna injinanku. A bari mai ya wuce!"

A cikin bayani nasa bai bayar da cikakkun bayanai game da yarjejeniyar ko yadda za a aiwatar da matakan ba.

"Tsagaita wuta nan-take kuma ta din-din-din"

Firaministan Pakistan, Shehbaz Sharif, ya sanar a safiyar Litinin cewa Amurka da Iran sun cim ma yarjejeniyar zaman lafiya bayan tattaunawa mai zurfi.

"Bayan tattaunawa mai zurfi, muna farin cikin sanar da cewa AN CIM MA Yarjejeniyar Zaman Lafiya tsakanin Amurka da Jamhuriyar Musulunci ta Iran," Sharif ya bayyana a wani rubutu a shafinsa na dandalin sada zumunta na Amurka X.

Ya ƙara da cewa "ɓangarorin biyu sun ayyana dakatar da dukkan ayyukan soja a dukkan fannoni nan-take kuma din-din-din , ciki har da a Lebanon."

A cewar Sharif, an tsara bikin sanya hannu a hukumance a ranar 19 ga Yuni a Switzerland.

Masu AlakaTRT Afrika - Yarjejeniyar Amurka da Iran ta ƙunshi sake buɗe Hormuz, taƙaita aikin nukiliya: babban jami'i a Iran