| Hausa
GABAS TA TSAKIYA
2 minti karatu
Iran ta ci gaba da aikin samar da gas a wurarenta uku na South Pars da ke cikin teku
South Pars, wanda Iran ke rabawa da Qatar, shi ne wurin samar da iskar gas mafi girma a duniya, kuma yana samar da mafi yawan iskar gas ɗin da Iran ke fitarwa.
Iran ta ci gaba da aikin samar da gas a wurarenta uku na South Pars da ke cikin teku
An dakatar da aiki a wuraren a kwanakin baya saboda hare-haren Amurka da Isra'ila / TRT Afrika Hausa

Iran ta ci gaba da aikin samar da gas a wurare uku na cikin teku da ke wuraren samar da gas na South Pars bayan an samu tsaiko na wani lokaci sakamakon illar da hare-haren Amurka da Isra’ila suka yi a wurarren sarrafa gas ɗin na Iran na kan tudu, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Iran ya ruwaito a ranar Lahadi.

Babban jami’in gudanarwa na Kamfanin Pars Oil and Gas, Touraj Dehqani, ya ce aikin dawo da samar da gas a wannan katafaren wuri iskar gas na ci gaba yadda ya kamata duk da matsalolin da aka fuskanta kwanan nan.

 “Dawo da samarwa da sarrafa iskar gas mai yalwa a wannan filin da muke rabawa da wata ƙasa yana tafiya yadda ya kamata,” in ji Dehqani, wanda ya danganta nasarar da “ƙwarewar masana’antar mai da iskar gas, ingantaccen tsarin samarwa da gudanarwa da kuma cikakken amfani da damar da ake da ita.”

Ya ƙara da cewa, “Ya zuwa yanzu, wurare uku na South Pars da ke cikin teku sun koma cikin tsarin samar da iskar gas.”

A cewar Dehqani, wasu wuraren da ke cikin teku waɗanda ke da alaƙa da matatun mai da suka lalace sun tilasta dakatar da aiki a lokacin yaƙin Amurka da Isra’ila, duk da cewa su kansu suna cikin cikakken yanayin aiki.

“Duk da kasancewarsu cikin cikakken shiri kuma ba tare da wata lalacewa ga kayayyakin da ke cikin teku ba, dole ne a dakatar da aikin samarwa saboda babu damar karɓa da sarrafa iskar gas ɗin da aka samar a cibiyoyin da ke kan tudu,” in ji shi.

South Pars, wanda Iran ke rabawa da Qatar, shi ne wurin samar da iskar gas mafi girma a duniya, kuma yana samar da mafi yawan iskar gas ɗin da Iran ke fitarwa. An fuskanci tangarda a wuraren gas ɗin bayan hare-haren da Isra’ila ta kai wa kayayyakin makamashi a yankin Assaluyeh a watan Maris.