| Hausa
NIJERIYA
6 minti karatu
Majalisar yaƙin neman zaɓen APC ta ƙaddamar da shirin samar da tsaro na Tinubu na shekaru biyar
Shirin ya ƙunshi tsarin da zai jagoranci manufofin tsaro na dogon lokaci, tare da daidaita buƙatun soji da ayyukan tsaro da kashe kuɗaɗe bisa la’akari da ƙalubalen tsaron da Nijeriya ke fuskanta a yanzu da kuma nan gaba.
Majalisar yaƙin neman zaɓen APC ta ƙaddamar da shirin samar da tsaro na Tinubu na shekaru biyar
Sabon shirin tsaro na APC na shekaru biyar na nuna wani gagarumin yunkuri na gwamnatin Nijeriya na karfafa matakan yaki da rashin tsaro. / Fadar Shugaban ƙasar Nijeriya

Majalisar Yaƙin Neman Zaɓen APC a Nijeriya ta sanar da wani sabon shirin tsaro na shekara biyar ƙarƙashin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da nufin magance rashin tsaro da ya daɗɗe yana addabar ƙasar, ta hanyar faɗaɗa ƙarfin sojoji da inganta tattara bayanan sirri da kuma daidaita ayyukan hukumomin tsaro.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Dele Alake, mai magana da yawun kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na Jam’iyyar APC, ya fitar a ranar Lahadi kan matakan da gwamnatin ke ɗauka wajen magance matsalar tsaro.

“Shugaba Bola Tinubu ya ƙuduri aniyar kawo ƙarshen matsalar rashin tsaro da ta kwashe shekaru 17 tana addabar sassan Nijeriya, ta hanyar aiwatar da cikakken tsarin dabarun tsaro na shekaru biyar,’’ in ji sanarwar.

Majalisar ta ce, “an tsara wannan shiri ne domin ƙarfafa tsarin tsaron ƙasar tare da inganta ayyukan sojoji da kuma tabbatar da ɗaukar matakan da suka dace ta hanyar haɗin gwiwa wajen tunkarar barazanar da ka iya tasowa.”

Haka kuma, sanarwar ta zo ne a daidai lokacin da gwamnati ke ikirarin cewa ayyukan soji a cikin shekaru uku da suka gabata sun kawar da ‘yanta’adda fiye da 15,000, ciki har da mambobin ƙungiyar Boko Haram.

Kazalika, gwamnatin ta ce fiye da mayaƙan Boko Haram da iyalansu 130,000 ne suka miƙa wuya ƙarƙashin shirin Operation Safe Corridor, wanda aka kafa domin gyara halayen tsoffin masu tada ƙayar baya da kuma taimaka musu su koma cikin al’umma.

Masu AlakaTRT Afrika - Sojojin Nijeriya sun kashe 'yanta'adda takwas, sun kuɓutar da mutum 125 da aka yi garkuwa da su

A cewar kwamitin, gwamnatin na amfani da dabaru guda biyu, wato ci gaba da kai hare-haren soji kan ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai da kuma aiwatar da shirye-shiryen da ba na yaƙi ba domin magance matsalar rashin tsaro.

Faɗaɗa ƙarfin soji da yawan jami’ai

A wani ɓangare na ƙoƙarin ƙarfafa rundunar sojin Nijeriya, Tinubu ya amince a kafa ƙarin rundunonin soji guda huɗu, lamarin da ya ƙara yawan rundunonin sojin ƙasar daga takwas zuwa 12.

Sabbin rundunonin, waɗanda za su kasance a Makurdi, Ilorin, Jalingo da Benin City, na da nufin rage cunkoson gudanar da ayyukan soji a wasu wurare, tare inganta tsarin jagoranci da sa ido da ƙarfafa tsaron iyakoki da kuma bai wa sojoji damar mayar da martani cikin gaggawa kan barazanar tsaro.

Shugaban ya kuma amince da ɗaukar ƙarin sojoji 28,000 domin ƙara yawan jami’an da ke aikin tabbatar da tsaro da kuma inganta ƙarfin rundunar wajen gudanar da ayyukanta.

Domin tallafa wa wannan shirin na ɗaukar sabbin sojoji, an amince da kafa ƙarin cibiyoyin horas da sojoji guda biyu a birnin Osogbo na Jihar Osun, da Amasiri-Edda na Jihar Ebonyi.

Kowace daga cikin cibiyar za ta iya horas da sabbin sojoji 6,000 a lokaci guda, wanda hakan zai kai adadin waɗanda za a iya horaswa a cibiyoyin biyu zuwa 12,000.

Kwamitin yaƙin neman zaɓen APC ya ce tuni sabbin dakaru 5,210 suka fara samun horo a cibiyar da ke Osogbo.

Haka kuma, Tinubu ya amince da ɗaukar ƙarin jami’an ’yansanda 50,000 domin ƙarfafa ayyukan rundunar da kuma inganta matakan daƙile laifuffuka a sassan ƙasar.

Baya ga ƙarin jami’an tsaro, gwamnatin na zuba jari a wajen gine-ginen gidajen sojoji da inganta walwalar jami’ai.

Masu AlakaTRT Afrika - An kashe mutum 418, an sace 227 a cikin wata biyu a Nijeriya, in ji rundunar 'yansandan ƙasar

Ɗaya daga cikin ayyukan shi ne gina barikin sojoji mai gidaje 700 a Ikere-Ekiti na Jihar Ekiti, domin samar wa jami’an soji ingantattun wuraren zama da kuma muhimman kayayyakin more rayuwa da za su taimaka musu wajen gudanar da ayyukansu.

Inganta bayanan sirri da haɗin gwiwar hukumomin tsaro

A ƙarƙashin sabon shirin tsaro na shekaru biyar, ana sa ran gwamnatin tarayya za ta ƙara mayar da hankali kan tattara bayanan sirri da sa ido, da amfani da fasahar zamani da kuma inganta haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro.

Shirin na da nufin tabbatar da cewa ana amfani da kuɗaɗen da ake warewa ɓangaren tsaro bisa la’akari da barazanar da ake fuskanta da kuma buƙatun ayyukan soji.

Haka kuma, ana sa ran zai taimaka wajen inganta shirin ko-ta-kwana na sojoji tare da cike giɓin kayan aiki da kuma rage almubazzaranci da kuɗaɗen gwamnati.

Wannan mataki ya biyo bayan umarnin da Tinubu ya bayar a watan Agustan 2026 na shirya cikakken nazari kan barazanar tsaron Nijeriya da kuma tsara ayyukan tsaro na shekaru biyar.

Shugaban ya kafa kwamitin mutum 11 ƙarƙashin jagorancin mai ba shi shawara kan harkokin tsaron cikin gida, Manjo Janar Adeyinka Famadewa, domin gano manyan barazanar tsaro, da tantance ƙarfin sojoji da kuma bayar da shawarwari kan abubuwan da ya kamata a mayar da hankali a kai.

An buƙaci kwamitin ya gabatar da rahotonsa da shawarwarin da ya tsara cikin kwanaki 90. Ana kuma sa ran tsarin zai zama jagora wajen tsara kasafin kudin tsaro da sayen kayan aikin soji a tsawon shekaru masu zuwa.

Matsalar rashin tsaro na ci gaba da zama babban kalubale

Duk da ikirarin gwamnatin na samun nasarori a ayyukan soji da karin zuba jari a bangaren tsaro, Nijeriya na ci gaba da fuskantar hare-haren ’yan tada kayar baya, da ’yanbindiga da sauran ƙungiyoyin masu aikata laifuffuka a sassa daban-daban na ƙasar.

Wasu alƙaluman tsaro na baya bayan nan sun nuna girman ƙalubalen da ƙasar ke fuskanta.

Rundunar ’yansandan Nijeriya ta ce an samu hare-hare wanda ya kai ga salwantar rayuka 418 da sace mutane 227 cikin tsawon makonni takwas a watan Satumba da Oktoban 2026.

Masu AlakaTRT Afrika - Rikicin Nijeriya ya tilasta wa dubban mutane tserewa zuwa Nijar: Majalisar Ɗinkin Duniya

Tasirin rikicin ya kuma ƙetare iyakokin ƙasar, inda hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNHCR) ta bayyana cewa kusan mutane 64,000 ne suka tsere daga gidajensu a arewacin Nijeriya zuwa maƙociyarta Nijar tun farkon shekarar 2026 sakamakon tashe-tashen hankula.

Ci gaba da aukuwar waɗannan hare-hare na ƙara janyo damuwa kan kariyar fararen-hula, da matsalar gudun hijira da kuma ƙarfin hukumomin tsaro na dawo da zaman lafiya mai ɗorewa a yankunan da abin ya shafa.

A ɓangare guda kuma, sabon shirin tsaron na nuna wani gagarumin yunƙuri na gwamnatin Nijeriya na ƙarfafa matakan yaƙi da rashin tsaro.

Sai dai nasarar shirin za ta dogara ne da yadda za a aiwatar da shi, da samar da isassun kuɗaɗen aiwatarwa, da musayar bayanan sirri tsakanin hukumomin tsaro da kuma yadda za a tabbatar da cewa ayyukan soji sun haifar da kariya mai ɗorewa ga fararen-hula.