| Hausa
TURKIYYA
4 minti karatu
Erdogan na so manyan ƙasashe su yi ƙaimi a yaƙi da sauyin yanayi, ya yi Allah-wadai da lalata Gaza
Erdogan ya bayyana haka ne a yayin buɗe taron shugabannin ƙasashe na COP31 a ranar Laraba, a Antalya, da ke kudancin ƙasar Turkiyya.
Erdogan na so manyan ƙasashe su yi ƙaimi a yaƙi da sauyin yanayi, ya yi Allah-wadai da lalata Gaza
Erdogan ya bayyana haka ne a yayin buɗe taron shugabannin ƙasashe na COP31 a ranar Laraba, a Antalya, da ke kudancin ƙasar Turkiyya. / AA

Shugaban ƙasar Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, ya bukaci ƙasashe masu arziki da su ɗauki ƙarin nauyi wajen rage hayakin da ke haddasa ɗumamar duniya, tare da samar da kuɗaɗen yaƙi da sauyin yanayi, yana mai jaddada cewa dole ne a sauƙaƙa samun waɗannan kuɗaɗe, a tabbatar da dorewarsu, kuma su dace da buƙatun ƙasashen da ke amfana da su.

Erdogan ya bayyana haka ne a yayin buɗe taron shugabannin ƙasashe na COP31 a ranar Laraba, a Antalya, da ke kudancin ƙasar Turkiyya.

Ya yi gargaɗin cewa duniya na fuskantar ƙalubale masu ƙaruwa, ciki har da ɗumamar duniya, raguwar halittu masu rai, yawan amfani da albarkatun ƙasa fiye da kima, barazana ga samar da abinci, da kuma ƙarin aukuwar bala'o'in da sauyin yanayi ke haddasawa.

Erdogan ya yi kira da a inganta hanyoyin samun kuɗaɗen tallafi, fasaha da horarwa, musamman ga ƙasashe mafi ƙarancin ci gaba da ƙananan ƙasashe tsibirai.

Ya ce: "Mun ɗauki ƙara fito da buƙatun ƙasashen tekun Pasifik fili da kuma ba su muhimmanci a matsayin babban nauyin da ya rataya a wuyanmu."

Da yake bayyana matakan da Turkiyya ke ɗauka kan sauyin yanayi, Erdogan ya ce ƙasar na ƙoƙarin rage hayakin da ke haddasa ɗumamar duniya a fannoni daban-daban, tun daga makamashi da masana'antu zuwa sufuri da noma, inda ta mayar da sauyin zuwa tattalin arziki mai tsafta da amfani da makamashi mai ɗorewa a matsayin babban fifiko.

Ya ƙara da cewa: "Wayewarmu ta ginu ne a kan mutunta yanayi, kuma duniya amana ce mai tsarki da ya kamata a kare tare da kiyaye ta."

Rage hayakin da ke haddasa ɗumamar duniya zuwa sifili

Erdogan ya sake jaddada aniyar Turkiyya na cimma burin fitar da hayakin da ke haddasa ɗumamar duniya zuwa sifili nan da shekarar 2053, yana mai cewa ƙasar na haɗa batun kare muhalli cikin shirye-shiryen ci gaba da manufofin samar da makamashi.

Da yake magana kan shirin Zero Waste da aka ƙaddamar a shekarar 2017, Erdogan ya ce yawan sharar da ake sake sarrafawa a Turkiyya ya tashi daga kusan kashi 13 cikin 100 zuwa kusan kashi 40 cikin 100 a ƙarshen shekarar 2025.

Ya ce ƙasar na da burin samun gagarumin ci gaba a fannoni 10 da ta ba fifiko, ciki har da sauya zuwa makamashi mai tsafta, rage shara, samar da isasshen abinci, bunƙasa masana'antu, gina birane masu jure sauyin yanayi da kuma kare tekuna.

Ya ƙara da cewa a cikin shekaru 10 masu zuwa, Turkiyya na da burin ƙara yawan amfani da wutar lantarki da kashi 50 cikin 100, rage saurin ƙaruwa wajen samar da shara da rabi, tare da faɗaɗa amfani da kayayyakin da za a iya sake sarrafawa a masana'antu.

Lalata muhalli a Gaza

Da ya juya kan halin da ake ciki a Gaza, Erdogan ya yi Allah-wadai da hare-haren Isra'ila, yana mai cewa sun haddasa mummunar lalata muhalli baya ga asarar rayukan jama'a.

Ya ce: "Kamar yadda na jaddada a jawabina ga babban zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, abin da ya faru a Gaza ba kisan ƙare-dangi ba ne kawai, har ma da lalata muhalli."

Ya yi nuni da yadda aka lalata itatuwan zaitun da suka shafe ƙarnuka, gurɓata ƙasa da ruwa, tare da mayar da birane gaba ɗaya kufai.

Erdogan ya kuma yi magana kan ƙara ta'azzarar matsalar jin ƙai bayan ruwan sama mai ƙarfi da ambaliyar ruwa da suka afku a yankin, inda ya ce an nutsar da dubban tantuna da matsugunan jama'a sakamakon lalacewar ababen more rayuwa.

Ya ce: "Daruruwan dubban 'yan'uwanmu a Gaza, waɗanda ba su da rufin da za su fake a ƙarƙashinsa, musamman yara marasa laifi da ke rawa da sanyi, na fama da rayuwa cikin ruwa a lokacin hunturu, galibi ba tare da iyayensu ba."

Erdogan ya jaddada cewa babu wanda ya san halin da ake ciki ko kuma ya shaida shi da zai iya guje wa alhakin da ke kansa.

Ya yi kira da a gaggauta kai kayan agajin jin ƙai zuwa Gaza, a kawo ƙarshen killace yankin, sannan a dakatar da wahalhalun da ake jefa Falasɗinawa a ciki.

Erdogan ya ce: "Nuna ƙarfi ta hanyar wahalar da yaran Gaza, a gaskiya, alama ce ta rauni, gazawa, kuma fiye da komai, rashin tausayi da imani."

Ya kammala da jaddada cewa wajibi ne a bar wa al'ummomin da za su zo nan gaba duniya mai tsafta, koren muhalli da adalci, kafin duniya ta zama wurin da ba za a iya rayuwa a cikinta ba.