Gwamnatin Nijar ta haramta fitar da gyaɗa zuwa ƙasashen waje, a wani mataki na tabbatar da wadatar gyada a kasuwannin cikin gida da kuma tallafa wa masana'antun sarrafa amfanin gona na ƙasar.
Ministan Kasuwanci da Masana'antu, Abdoulaye Seydou, ne ya sanar da matakin a ranar Juma'a yayin wani taron manema labarai a birnin Yamai, babban birnin ƙasar.
Matakin, wanda aka tabbatar ta hanyar wata doka mai ɗauke da kwanan wata 11 ga Nuwamban 2026, na da nufin kare muradun masu sayen gyada a cikin gida, tabbatar da wadatarta a kasuwanni da kuma samar da isassun kayayyakin sarrafawa ga masana'antun sarrafa gyada na ƙasar.
Sai dai Seydou ya bayyana cewa gwamnati na iya bayar da izinin fitar da gyada zuwa ƙasashen ƙungiyar ƙasashen ƙawancen Sahel (AES) a wani yanayi na musamman, bisa wasu ƙa'idojin da aka tsara.
Ya yi gargaɗin cewa duk wanda ya yi ƙoƙarin fitar da gyaɗa zuwa ƙasashen waje ba tare da izini ba, hukumomin gwamnati za su ƙwace kayan, inda jami'an kwastam da jami'an tsaro za su tabbatar da aiwatar da dokar.
Ministan ya ce matakin na cikin ƙoƙarin da gwamnatin Nijar ke yi na ƙarfafa 'yancin cin gashin kan tattalin arziƙin ƙasar, ta hanyar bunƙasa noman amfanin gona da sarrafa shi a cikin gida.
Ya kuma buƙaci hukumomin gwamnati, jami'o'i, barikokin sojoji da sauran cibiyoyin gwamnati da su ba kayayyakin da ake ƙerawa a cikin gida fifiko wajen saye da samar da kayayyakin da suke buƙata.






















