Jami'an rundunar tsaron Nijar sun ƙwace wasu makamai da alburusai masu yawa da ake zargin an shirya kai wa ‘yanta’addan Boko Haram a yankin Diffa da ke kudu maso gabashin ƙasar, kamar yadda rahoton ayyukan tsaro na tsakanin 1 zuwa 12 ga Nuwamban 2025 ya bayyana.
Rahoton ya ce rundunar tsaron ƙasa ta Nijar ta ƙwato makaman harba rokoki kirar RPG-7 guda 12, da rokoki guda 11 da kuma alburusai iri-iri yayin wani samame da ta gudanar a Kablewa da ke yankin N'Guigmi, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasar ya rawaito.
An ce ƙwace makaman na daga cikin ayyukan tsaro da ake gudanarwa domin tarwatsa hanyoyin safarar makamai ba bisa ƙa'ida ba, tare da hana makaman shiga hannun ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai da ke yankin Tafkin Chadi.

Yankin Diffa, wanda ke iyaka da Nijeriya da Chadi, ya daɗe yana fama da matsalar rashin tsaro da ke da alaƙa da Boko Haram da sauran ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai.
Hare-hare da kuma zirga-zirgar mayakan ta kan iyakoki na ci gaba da zama babban ƙalubale ga jami'an tsaro a yankin.
Ƙwace makaman na baya-bayan nan ya sake jaddada damuwar da ake da ita kan safarar makamai a yankin Sahel da Tafkin Chadi, inda ƙananan tsauraran matakan tsaro a wasu sassan iyakoki ke bai wa ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai damar amfani da hanyoyin safarar makamai.
Jami'an tsaron Nijar sun ƙara ƙaimi wajen gudanar da ayyuka a yankunan da matsalar ta fi ƙamari, yayin da hukumomi ke ƙoƙarin shawo kan ayyukan mayakan da kuma ƙarfafa sa ido a kan iyakokin ƙasar.
Sai dai hukumomin ba su bayar da ƙarin bayani kan waɗanda ake zargin sun samar da makaman ko kuma kama wasu mutane dangane da ƙwace makaman ba.





















