| Hausa
GABAS TA TSAKIYA
2 minti karatu
Rundunar sojin Isra'ila ta yi ikirarin kashe shugaban rundunar sojin Hamas a wani babban hari a Gaza
Rundunar sojin ta ce ta kashe Mohammed Awda a harin da aka kai Gabashin Gaza,amma har yanzu kungiyar Falasdinawa ta Hamasa ba ta ce komai ba.
Rundunar sojin Isra'ila ta yi ikirarin kashe shugaban rundunar sojin Hamas a wani babban hari a Gaza
Rundun sojin Isra'ila ta yi ikirarin kashe shugaban rundunar sojin Hamas a wani babban hari a Gaza / Reuters

Sojojin Isra'ila sun bayyana cewa sun kashe Mohammed Awda a wani harin sama a arewacin Gaza, suna zargin cewa shi ne wanda aka zaɓa a matsayin sabon kwamandan reshen sojin ƙungiyar Falasdinu ta Hamas.

Wannan ikirari na ranar Laraba ya biyo bayan mummunan harin sama na Isra'ila da ya afka wa wani yanki mai cunkoso a tsakiyar birnin Gaza a daren Sallah Babba, inda aka kashe wata Bafalasdiniya kuma wasu suka ji rauni, a cewar majiyoyin kiwon lafiya.

Babu wani bayani daga Hamas ko reshen sojinta na Qassam, game da wannan ikirarin na Isra'ila.

A ranar Talata, Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da Ministan Tsaro Israel Katz sun ce sojoji wani harin sama Awda a birnin Gaza.

Wadannan zargin na Isra'ila sun fito ne a daidai lokacin da masu sharhi daga Isra'ila da 'yan adawa ke ƙara yin gargaɗi cewa Netanyahu na iya neman ta’azzara tashin hankali a Gaza domin dalilan siyasa, ciki har da yiyuwar rushe Knesset da gudanar da zaɓe na gaggawa.

Tun daga Oktoban 2023, a cikin shekaru biyu na mummunan farmaki, Isra'ila ta kashe fiye da mutane 72,000 kuma ta jikkata sama da 172,000, inda har ila yau farmakin ya haifar da barnar da ta shafi kashi 90 cikin ɗari na manyan ababen more rayuwar farar hula, kafin a sanar da tsagaitawar wuta a watan Oktoba da ya gabata.