| Hausa
NIJERIYA
3 minti karatu
Wasu sun nemi na mutu saboda tallafin mai da canjin dala— Tinubu
Shugaban Nijeriya Bola Tinubu a ranar Laraba ya bayyana cewa wasu mutane da suka fi kowa amfana daga tsarin tallafin mai da tallafin dala suna fatan ya mutu, biyo bayan tsare-tsaren da ya gabatar lokacin da ya hau ƙaragar mulki a shekarar 2023.
Wasu sun nemi na mutu saboda tallafin mai da canjin dala— Tinubu
Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu. / AP / AP

Shugaban Nijeriya Bola Tinubu a ranar Laraba ya bayyana cewa wasu mutane da suka fi kowa amfana daga tsarin tallafin mai da tallafin dala suna fatan ya mutu, biyo bayan tsare-tsaren da ya gabatar lokacin da ya hau ƙaragar mulki a shekarar 2023.

Shugaban ya yi magana ne a wani taron da manyan ‘yan Nijeriya da masu ruwa da tsaki da suka yi gwagwarmayar kawo ƙarshen mulkin soji domin dawo da mulkin farar-hula a ƙasar suka yi domin tunawa da gwagwarmayar bayan shekara 32, suna masu cewa dole a tabbatar da tsarin dimokuraɗiyya a Nijeriya.

Ɗaya daga cikin hanyoyin tabbatar da ɗorewar tsarin dimokuraɗiyyar ita ce yaba wa waɗanda suka taka rawar gani a gwagwarmayar, ko suna raye ne ko kuma sun rasu, a cewar ‘yan gwagwarmayar.

Waɗanda suka gabatar da jawabai a wurin a ranar Laraba sun haɗa da wakilim Shugaba Tinubu, tsohon gwamnan jihar Ogun, Aremo Olusegun Osoba da shararren marubucin Nijeriya da ya ci kyautar Nobel, Farfesa Wole Soyinka.

Waɗanda suka fi cin moriyar tallafin mai da na dala na ruruta tashin hankali

Da yake gabatar da jawabi a amdadin Tinubu, Olusegun Osoba ya ce: “Game da tsaro, Shugaban Kasa ya ce na sanar da ku cewa yana sane cewa akwai ƙoƙari da gangan na gurgunta zaman lafiyar ƙasar daga wasu mutanen da shi ya san cewa ya yi wa laifi ta hanyar soke tsarin matakai na kasuwar musayar kudi da kuma soke tallafin mai.

“Ya ce waɗannan gungun mutanen da ke samun riba mai yawa ta hanyar sayar da dalar da suka sayo a farashin gwamnati a kasuwar bayan fage za su nemi ya mutu a ko wane lokaci, amma shi ya lashi takobin cewa idan wannan shi ne abin da zai iya yi kawai, shi zai tabbatar da cewa ya sake fasalin tattalin arzikin Nijeriya.

“Ko ma mene ne, ya lashi takobin fuskantarsa . Saboda haka wannan shi ne sako daga shugaban ƙasa .”

Ku saurari ingantaccen sakamako a wa’adina na biyu – Tinubu

Osoba ya ce shugaban ya yaba wa NADECO da gwagwarmayar, kuma ya ce shi ba zai kasance a ƙaragar mulki ba idan ba dan NADECO ba, kuma ya ɗauki alƙawarin ƙara aiki a wa’adinsa na biyu, idan aka sake zaɓansa .

Osoba ya ce : “Shugaban ƙasa ya ce na sanar da ku cewa shi yana tare da ku 100 bisa 100 , kuma har yanzu yana ba ku babbar girmamawa cewa da a yanzu ba ya inda yake a yau idan ba don dukkanku da kuka yi yaƙin tabbatar da dimokuraɗiyya ba.’’

Mayar da hankali kan tattalin arziki da tsaro a halin yanzu

A lokacin da yake ci gaba da jawabi, Osoba ya ce : “Ya ce shi yana cike da godiya ga abin da kuka yi domin kawo ƙasar nan inda muke a yau, kuma ya neme ni na gaya muku cewa, da yawa daga cikin abubuwan da kuke neman ya yi zai ƙaddamar da wasu daga cikin waɗannnan lamurran na siyasa idan ya samu wa’adi na biyu. Ya ce muhimmin batun da ke gabansa a halin yanzu shi ne tattalin arziki da tsaro.

“Dukkanku za ku iya ganin cewa lamarin tsaro a halin yanzu yana tafiya a hankali zuwa yankin kudu maso yammaci. Saboda haka ya ce muhimmin abu na farko da yake fuskanta a halin yanzu shi ne tattalin arziki, kuma dukkanku za ku iya ganin cewa bambancin da ke tsakanin kasuwar bayan fage da kasuwar gwamnati ta musayar kuɗi kusan sifili ne a yanzu.

Kudin naira, wanda suka yi tunanin cewa zai kai N2,000 ga kowace dala 1 a halin yanzu yana kusan 1,380 ko makamancin hakan.