| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
Rundunar Sojin Amurka da ke aiki a Afirka ta ƙara kai sabbin hare-hare kan 'yanta'adda a Nijeriya
Tinubu ya ce dakarun Nijeriya sun yi aiki kafaɗa da kafaɗa da rundunar sojin Amurka a wani abin da ya kira aikin hadin gwiwa mai jarumta wanda ya yi babbar illa ga ‘yanta'addan.
Rundunar Sojin Amurka da ke aiki a Afirka ta ƙara kai sabbin hare-hare kan 'yanta'adda a Nijeriya
Amurka ta tura daruruwan sojoji zuwa Nijeriya a kwanakin baya domin tallafawa da kuma horar da dakarun kasar. / AA

Rundunar Sojin Amurka da ke aiki a Afirka (AFRICOM) ta ce ta kai wasu hare‑haren jiragen sama kan 'yanta'adda a arewa maso gabashin Nijeriya a ranar Lahadi tare da hadin gwiwar gwamnatin Nijeriya.

Babu wani sojan Amurka ko na Nijeriya da ya ji rauni yayin hare-haren, in ji AFRICOM a ranar Litinin.

A ranar Asabar, sojojin Amurka da na Nijeriya sun yi wani aiki da ya kashe Abu-Bilal al-Minuki, babban jagoran kungiyar ta'addanci ta Daesh, a arewa maso gabashin Nijeriya, in ji Shugaban Amurka Donald Trump da takwaransa na Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu.

Tinubu ya ce dakarun Nijeriya sun yi aiki kafaɗa da kafaɗa da rundunar sojin Amurka a wani abin da ya kira aikin hadin gwiwa mai jarumta wanda ya yi babbar illa ga ‘yanta'addan.

‘Muna godiya da hadin kai’

Trump, wanda a baya ya zargi Nijeriya da kasa kare Kiristoci daga 'yanta'adda, ya gode wa gwamnatin Nijeriya saboda hadin kai a aikin.

Nijeriya na fafatawa da ƙungiyoyin ta'addanci, ciki har da rassan yankin na ƙungiyar Daesh da Boko Haram. Haka kuma ta kai hare-hare da ayyukan soja kan ‘yan fashin daji waɗanda ke satar mutane don neman kuɗin fansa.

A 'yan kwanakin nan Amurka ta tura ɗaruruwan sojoji zuwa Nijeriya don tallafawa da horar da rundunoninta bayan tashin hankali tsakanin ƙasashen biyu.