Wata sabuwar ɓarkewar cutar Ebola a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kongo ta kashe fiye da mutum 80 yayin da hukumomi suka yi gargaɗin cewa babu rigakafi ga wannan nau'in, inda Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ayyana matsalar a matsayin matsalar lafiya ta gaggawa ta ƙasa da ƙasa a ranar Lahadi.
An bayar da rahoton mutuwar mutane 88 da kuma adadin mutum 336 da ake zargin sun kamu da wannan mummunan zazzabin na zubar da jini mai yaɗuwa, in ji Cibiyar Kula da Cututtuka da Rigakafi ta Afirka (CDC Africa) a cikin wni sabon rahotonta a ranar Asabar.
Hukumar WHO mai hedkwata a Geneva ta ce ɓarkewar cutar da nau'in Bundibugyo ke haifarwa ya zama matsalar kiwon lafiya ta gaggawa da ta shafi ƙasa da ƙasa.
Wannan shi ne mataki na biyu mafi girma na gargaɗi a karkashin dokokin lafiya na ƙasa da ƙasa.
Hukumar Lafiya ta Duniyar ta yi gargaɗi cewa ba a san ainihin girman adadin waɗanda ake zargi sun kamu da cutar ba, amma ta tsaya kan cewa zuwa yanzu ba za ta ayyana cutar a matsayin annoba ba — wadda ita ce matakin gargaɗi mafi girma da aka ɓullo da shi a 2024.
'Babu rigakafi, babu magani’
Kungiyar Agajin Likitoci ta Doctors Without Borders (MSF) ta ce tana shirin “taimako mai girma”, inda ta bayyana saurin yaɗuwar cutar a matsayin “abin matukar damuwa”, a cikin gargaɗin da hukumomi suka jaddada.
"Nau'in Bundibugyo ba shi da rigakafi, ba shi da wani magani na musamman," in ji Ministan Lafiya na DRC, Samuel-Roger Kamba.
"Wannan nau'in na kisa matuƙa, wanda zai iya kaiwa kashi 50%."
An fara gano wannan nau'in a 2007, kuma ya kashe wani ɗan ƙasar Kongo a ƙasar Uganda mai maƙwabtaka, in ji jami'ai a ranar Asabar.
Ana samun rigakafin Ebola ne kawai ga nau'in Zaire, wanda aka gano a 1976 kuma ke da mace-macen da suka fi yawa tsakanin kaso 60 zuwa 90.
Hukumomin lafiya sun tabbatar da sabuwar ɓarkewar a ranar Juma'a a lardin Ituri a arewa maso gabashin DRC, wanda ke iyaka da Uganda da Kudancin Sudan, a cewar CDC Africa.










