Shugaba Bola Tinubu ya isa Nairobi babban birnin ƙasar Kenya, domin halartar taron Afirka da Faransa wanda aka shirya farawa a ranar 11 ga Mayu.
Shugaba Tinubu ya isa Nairobin daga birnin Paris na Faransa a ranar Litinin, inda manyan jami’an gwamnatin Nijeriya suka tarbe shi a Filin Jirgin Sama na Jomo Kenyatta International (JKIA).
Jami’an da suka tarbe shi sun haɗa da; Ministan Kuɗi kuma Mai Kula da Harkokin Tattalin Arziƙi, Mista Taiwo Oyedele; Ministar Harkokin Waje, Bianca-Odumegwu Ojukwu; Karamin Ministan Harkokin Waje, Ambasada Sola Enikanolaiye; Ministan Noma da Abinci, Sanata Abubakar Kyari; Ministan Muhalli, Balarabe Lawal; Ministar Masana’antu, Kasuwanci da Zuba Jari, Dokta Jumoke Oduwole; da Ministan Harkokin Ruwa da Tattalin Arziƙin Ruwa, Adegboyega Oyetola, da sauransu.
Shugaban na Nijeriya yana halartar taron ne wanda ake gudanarwa a Cibiyar Taro ta Kenyatta International Convention Centre (KICC) da ke Nairobi, tare da shugabannin ƙasashen Afirka fiye da 30.
Ana sa ran taron, wanda Shugaban Faransa Emmanuel Macron da Shugaban Kenya William Ruto ke jagoranta tare, zai nuna kudirin Nijeriya na ƙarfafa haɗin gwiwar dabaru da ƙasashen Afirka da kuma Jamhuriyar Faransa.
Taron Kenya da Faransa na mayar da hankali ne kan manyan batutuwa da suka haɗa da sauyin makamashi, zamanantar da masana’antu, komawa kan fasahar zamani ta dijital, gyaran tsarin kuɗi na duniya, da matakan yaƙi da sauyin yanayi.
Taron ya kasance shi ne irinsa na farko da wata kasa wadda ba rainon Faransa ba ta karbi baƙuncinsa, inda masu sharhi ke cewa alamu ne da ke nuna yadda Faransar ke karkata wurin ƙasashen rainon Ingila bayan an tilasta wa Faransar janye sojojinta daga ƙasashen Afirka da dama da ta mulka.
Masu sharhi suna ganin shigar Nijeriya irin wannan taron wadda ita ce ƙsar Afirka mafi girman tattalin arziƙi ya nuna yadda Faransar ke ta ƙoƙarin ganin sai ta samo sabbin ƙawayea nahiyar.
Haka kuma masana na gargaɗin duk da cewa taron zai mayar da hankali ne kan abubuwa na ci gaba da haɗin gwiwa, akwai buƙatar a yi taka-tsantsan don kar Faransar ta yi amfani da hanyoyin da ta bi wurin tafiyar da ƙasashen Afirka da dama a tsawon shekaru.
Taron shugabannin kamfanonin Afirka
Bayan kammala taron Nairobi, ana sa ran Shugaba Tinubu zai wuce Kigali, Rwanda, domin halartar taron shekara-shekara na Africa CEO Forum wato taron shugabannin kamfanoni da manyan masu zuba jari na Afirka wanda aka shirya gudanarwa a ranakun 14 da 15 ga Mayu.
Taron mai taken “Scale or Fail,” ana kallonsa a matsayin mafi girman taron shugabannin kamfanoni masu zaman kansu, masu zuba jari, da masu tsara manufofi a Afirka, inda tattaunawar za ta mayar da hankali kan hanzarta sauyin tattalin arziƙin Afirka ta hanyar haɗin kan yankuna, bunƙasa masana’antu tare, da faɗaɗa zuba jari tsakanin ƙasashe.











