| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
Dakarun Nijeriya sun kashe 'yanta'adda a Jihar Zamfara
Yayin da sojoji suka yi nasarar kashe wasu daga cikin 'yanta'addar, masu tayar da ƙayar bayan sun harbe wasu daga cikin mutanen gari.
Dakarun Nijeriya sun kashe 'yanta'adda a Jihar Zamfara
Babban hafsan sojin ƙasa na Nijeriya, Laftanar Janar Waidi Shaibu / Nigerian army

Dakarun rundunar sojin Nijeriya na musamman, Operation Fansan Yamma, sun yi nasarar kashe ‘yan ta’adda biyu a Jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin ƙasar.

Wata sanarwa da jami’in watsa labarai na rundunar Laftanar Kanal Aliyu Danja ya fitar ta ce lamarin ya auku ranar Litinin a jerin samame da dakarun suka kai wasu wurare ciki har da ƙauyukan Maikwanuga ( a ƙaramar hukumar Talata Mafara ), da Aljumma da Gidan Dawa da Magami Didi da kuma Tungar Magaji (a ƙaramar hukumar Maradun).

“Yayin tafiyar, dakaru sun yi arangama da ‘yanta’adda a Tungar Magaji inda suka fi ƙarfinsu, kuma suka kashe ‘yanta’adda 2 kuma suka tilasta wa sauransu tserewa a gigice,” in ji sanarwar.

“Biyo bayan arangamar, dakarun sun gudanar da bincike a wurin, inda suka samo wata bindiga ƙirar AK-47 da kuma gidan harsashi cike da harsasai 30 da kuma babur ɗaya,” in ji shi .

Wannan na zuwa ne cikin ‘yan kwanaki bayan rundunar ta yi nasarar kashe ‘yanta’adda tara a jihohin Zamfara da Katsina a arewa maso yammacin ƙasar.

Harbe wasu daga cikin mutanen gari

Sai dai kuma wasu rahotanni daga yankin na Nijeriya na cewa ‘yan ta’adda sun kashe kimanin mutum 24 a hare-haren da suka kai garuruwan Jiƙamshi da Gwalgwaro a ƙananan hukumomin Musawa da Kankia na jihar Katsina.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa harin na baya bayan nan ya auku ne da yammacin ranar Litinin a kasuwar Jikamshi, inda aka harbe mutum bakwai yayin da mutane ke kammala harkokinsu na kasuwa ranar.

Jaridar ta ce harin ya faru ne yayin da sojosji suka yi nasarar kashe ‘yanta’adda 45 yayin musayar wuta a ƙaramar hukumar Danmusa ta jihar Katsina.

Jaridar ta ambato wani shaida yana cewa kimanin ‘yanbindiga 15 bisa babur ne suka afka wa kasuwar kuma suka buɗe wuta tare da satar kayayyaki da ƙimarsu ta kai miliyoyin naira.

A wani harin na daban da suka kai a ƙarshen mako, ‘yanta’addan sun kashe kimanin mazauna ƙauyen Gwalgoro 17 a ƙaramar hukumar Kankia. Jaridar ta ruwaito cewar mata da ƙananan yara sun tsere daga wurin sakamakon harin da ya auku ranar Asabar.

Yayin da gwamnatin jihar Katsina ke cewa mutum 11 ne aka kashe a harin, mazauna wurin na cewa mutum 17 aka kashe, in ji jaridar.