| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
Dangote ya sanar da shirinsa na samar da megawat 20,000 na wutar lantarki a Nijeriya
“A yanzu za mu shiga fannin lantarki… inda za mu samar da mewagat 20,000 ,” in ji Dangote, yana mai ƙarawa da cewa babu abin da Afirka ta fi buƙata kamar makamashi da takin zamani da abubuwan aiki a masana’antu.
Dangote ya sanar da shirinsa na samar da megawat 20,000  na wutar lantarki a Nijeriya
Aliko Dangote ya daɗe yana cewa 'yan Afirka ne ya kamata su bi sahun gaba wajen zuba jari a nahiyar / TRT Afrika English

Aliko Dangote, attajirin da ya gina rukunin masana’antu mafi girma a Afirka, ya ce zai mayar da hankali a fannin lantarkin Nijeriya inda aka shafe shekaru aru-aru ana fama da ƙarancin lantarki.

Attatijin ya sanar da wani gagarumin shiri na samar da wutar lantarki da ta kai megawat 20,000.

Wannan sanarwa na zuwa ne a daidai lokacin da ƙasar da ta fi yawan mutane a nahiyar Afirka ke fama da ƙarancin lantarki da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa lamarin da ke mummunan tasirin a fannin ci-gabanta.

Bayanin da ya yi yayin tattaunawa da babban daraktan hukumar da ke kula da ‘yan kasuwa a ƙasashe masu tasowa a Bankin Duniya (IFC), Makhtar Diop, wani mataki ne da ke nuna ƙara faɗaɗa tasirin masana’antun Dangote a wani fanni na daban bayan tace mai da siminti da takin zamani.

“A yanzu za mu shiga fannin lantarki… mu samar da mewagat 20,000,” in ji shi, yana mai ƙarawa da cewa babban abin da Afirka ta fi buƙata shi ne makamashi da takin zamani da ababen aiki na masana’antu.

Bayan ya ƙaddamar da matatar mai da ke iya tace gangar ɗanyen mai 650,000 a ko wace rana da kuma tabbatar da matsayi mai ƙarfi a kasuwar taki, Dangote ya nuna cewa rukunin kamfanoninsa na da kuɗi da kadararorin da zai iya amfani da su wajen magance matsalar fannin lantarki.

Shelar da Dangote ya yi ta shiga fannin samar da lantarki ta biyo bayan jerin gaza cika alƙawura ne daga gwamnatin Nijeriya.

Adebayo Adelabu, tsohon ministan makamashin Nijeriya ya gaza cika alƙawuran da ya yi cikin wa’adin da ya fitar da kansa na daidaita wutar lantarkin ƙasa a kan megawat 6,000.

Tun da ya zama minista a watan Agustan shekarar 2023, sau uku Adelabu yana bayar da wa’adi na gyara harkar wutar lantarki ba tare da ya cim ma alƙawarin da ya yi ba inda a yawancin lokuta wutar lantarkin da ake samarwa ba ta wuce megawat 3,331.

Kafin zuwan gwamnatin Shugaba Tinubu, gwamnatoci da dama sun sha yin alwashin samar da hasken lantarki a Nijeriya amma lamarin ya ci tura duk da biliyoyin dala da suke kashe a fannin.

Masana na cewa wutar lantarki ta gagari Nijeriya ne sakamakon matsanancin cin hanci da rashawa da suka yi wa fannin dabaibayi.

Sun ƙara da cewa muddin ‘yan kasuwa irin su Dangote suka zuba jari a fannin lantarki, ƙasar za ta samar da ci-gaba mai ɗorewa.