Tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Dijital na Nijeriya, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, ya sake jaddada matsayarsa ta goyon bayan tsarin direct primaries, wato ƙato-bayan-ƙato, wajen fidda ‘yan takarar jam’iyyar APC, yana mai cewa wannan ce hanya mafi dacewa da dimokuradiyya da adalci.
A wata hira da BBC Hausa, Farfesa Pantami ya bayyana cewa tun farko abin da suka tsaya a kai shi ne a gudanar da zaɓen fidda gwani kai tsaye, kuma ya yi farin ciki da yadda Shugaban Kasa, da jam’iyyar APC ta ƙasa da kuma ta jiha suka amince da hakan.
“Na ji daɗin maganar da Shugaban Kasa (Bola Tinubu) ya yi cewa bai yarda a yi kama-karya ba. Wannan magana ya kira ni da kansa ya gaya min babu shamaki. Na biyu, Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nantawe, ya ce bai yarda a yi kama-karya ba. Wannan abu da suka yi sun cancanci a yaba musu. Mu ba so muke a bata ba, muna so ne a yaƙi zalunci, kuma ko don mu aka yi shi, za mu yaƙe shi,” in ji shi.
Sai dai ya jaddada cewa babban ƙalubale a yanzu shi ne yadda za a gudanar da zaɓen cikin gaskiya da adalci. A cewarsa, idan aka yi adalci, jam’iyyar APC za ta samu nasara, amma idan aka yi zalunci, hakan na iya jefa harkokin siyasa cikin ruɗani.
Pantami ya yi gargadin cewa Allah ba ya goyon bayan zalunci, yana mai cewa ko da shi ne aka yi wa gata ta hanyar zalunci, ba zai amfane shi ba. Ya ƙara da cewa shiru da ake yi a kan zalunci shi ne ya jawo matsaloli da dama a Nijeriya.
Ya bayyana cewa ba ya gaba da kowa, amma yana yaƙar zalunci ne saboda yadda yake ganin hakan na barazana ga dimokuradiyya.
“Ba na faɗa da kowa, amma ina faɗa da zalunci. Zalunci na gani shi ya sa nake yaƙarsa, kuma ko sanadin raina zai yi, babu gudu babu ja da baya,” in ji shi.
Ya ce da a ce komai yana tafiya daidai a Nijeriya, sannan babu wata matsala a Arewacin ƙasar, da babu abin da ya haɗa shi da siyasa.
Dangane da goyon bayan jama’a, Pantami ya ce ba shi da fargaba ko a Jihar Gombe ko a duk Arewacin Nijeriya, yana mai cewa masu tsoron tsarin ƙato-bayan-ƙato su ne waɗanda ba su da goyon bayan talakawa.
Ya ƙara da cewa duk ɗan siyasar da yake da yakinin talakawa na tare da shi, ba zai ji tsoron wannan tsari ba, illa kawai ya nemi a tabbatar da adalci.
“Abin da nake faɗa ba da baki ba ne. Za ka ga yaƙi da zalunci da ba ka taɓa ganin irinsa ba a Nijeriya. Lokaci zai yi ka gani. Yaƙin zalunci da nake nufi za a yi shi ta hanyar bin matakan shari’a ne, bisa ƙa’ida da dokokin ƙasa,” in ji shi.
Da aka tambaye shi ko zai sauya jam’iyya idan ba a masa adalci ba a APC, Pantami ya ce suna da matakai guda uku da suke dubawa, amma lokaci bai yi da za su bayyana su ba. Duk da haka, ya jaddada cewa har yanzu shi cikakken ɗan jam’iyyar APC ne.














