A maraicen Larabar nan ne za a yi karawa ta biyu tsakanin Bayern Munich da Paris Saint-Germain don fayyace kulob ɗin da zai je wasan ƙarshe na Gasar Zakarun Turai na kakar 2025/26.
Za a yi wasan a Jamus, gidan Bayern, bayan da zagayen farko da ya gudana a Paris ya ɗauki hankali matuƙa, saboda ruwan ƙwallaye da aka gani daga dukkan ɓangaororin biyu.
PSG ta yi nasara da ci 5-4, wanda ya janyo wasan ya zama wasa mafi yawan zura ƙwallaye a matakin dab-da-na-ƙarshe a tarihin gasar.
Yayin da ake dakon wasan da zai fayyace ƙungiyar da za ta kara da Arsenal a wasan ƙarshe, babu ƙungiya guda da ta nuna alamar za ta yi wani babban sauyi a salon wasanta.
A wasan farko, masana ƙwallo sun soki ‘yanwasan baya na duka ƙungiyoyin ganin yadda suka bari aka zura ƙwallaye har tara a irin wasa mai muhimmanci kamar na semifainal.
Kocin PSG, Luis Enrique ya ce ba za su tsaya ƙoƙarin kare fifikon ƙwallo ɗaya da suke ita ba daga wasan farko, duk da ya san cewa ko canjaras aka tashi zai wadaci PSG wucewa gaba.
Enrique ya ce, "Karawa da Bayern, ba ma buƙatar canja komai saboda burinmu shi ne mu ci wasan… Wasa ne tsakanin mafi kyawun ƙungiyoyi a Turai."
Shi ma kocin Bayern, Vincent Kompany, ya ce za su fito da shirinsu kuma ya jaddada cewa bai ga dalilin sauya salon taka leda a wasan ba.
"Idan na ce tabbas za mu yi wani abu daban, hakan ba zai zama amsa mai kyau ba," in ji Kompany.
Bayan wasan samifainal ɗin, Arsenal ta Ingila za ta san ƙungiyar da za ta kara da ita a wasan ƙarshe na kofin wanda za a buga a birnin Budapest, ranar 30 ga Mayun 2026.








