| Hausa
GABAS TA TSAKIYA
2 minti karatu
Bayanan sirri na Amurka sun nuna cewa Iran na da iko da makamai masu linazami masu ƙarfi - Rahoto
Bayan sirri sun nuna cewa Tehran ta samu damar kai ga yawancin wuraren makamai masu linazaminta, ciki harda 30 daga cikin wuararen makamai masu linzaminta 33 a bakin mashigin ruwan Hormuz.
Bayanan sirri na Amurka sun nuna cewa Iran na da iko da makamai masu linazami masu ƙarfi - Rahoto
Bayanan leƙan asirin Amurka: Iran na da 70% tarin makamai masu linzamin da ta ke da su kafin yaƙi da rokokin harbin tafi da gidanka. (Tsohon hoto / AA / AA

Ɓoyayyun bayanan sirrin Amurka sun nuna cewa Iran tana da mai yawa daga cikin ikonta na makamai masu linzami duk da iƙirarin da gwamnatin Trump ke yi cewa ta yi “kaca-kaca” da sojin Tehran, in ji wani rahiton wata kafar watsa labaran Amurka .

Jaridar The New York Times ta ba da rahoton cewa bayanan sirrin da aka tattara daga farkon watan Mayu sun nuna cewa Iran ta sake samun damar aiki da yawancin wuraren makamai masu linzaminta , ciki har da wuraren makamai masu linzami 30 daga cikin 33 da ke bakin Mashigin Ruwan Hormuz.

Da take ishara ga mutane da ke da masaniya game da bayanan, jaridar ta ce har yanzu Iran na da kimanin kashi 70 cikin 100 na tarin makamai masu linzaminta da ababen harba makaman da take da su kafin a fara yaƙi.

Bayanan da aka tattara kuma sun gano cewa kashi 90 cikin 100 na wuraren ajiyar makamai masu linzami na Iran na ƙarƙashin ƙasa da ababen harba makaman a halin yanzu “suna iya aiki gabaɗaya ko kuma wasu ɓangarorinsu na iya aiki.”

“Abin da ba zai ɗore ba ”

An ambato mai magana da yawun Fadar White House Olivia Wales tana cewa gwamnatin Iran ta san cewa “zahirinta na yanzu ba zai ɗore ba” kuma duk wanda ke “tunanin cewa Iran ta sake tsara sojinta yana yaudarar kansa ne ko kuma baki [ne]” na rundunar kare juyin juya halin Iran (IRGC).

Tashin hankali na yanki ya ƙaru tun da Amurka da Isra’ila suka ƙaddamar da hare-hare kan Iran ranar 28 ga watan Fabrairu, lamarin da ya haddasa ramuwar gayya daga Tehran kan Isra’ila da ƙawayen Amurka a ƙasashen Larabawa da ke gaɓar teku, da kuma rufe mashigin ruwan Hormuz.

An fara wani tsagaita wuta na mako biyu ranar 8 ga watan Afrilu ta hanyar shiga tsakanin Pakistan, amman tattaunawar da aka yi daga baya a Islamabad ta gaza samar da yarjejeniya mai ɗorewa.

Daga bayan Trump ya tsawaita tsagaita wutan na sai baba ta gani. Tun wancan lokacin, Islamabad tana aiki domin sake farfaɗo da diflomasiyyar da ta kafe.

Trump ya yi watsi da martani na baya bayan nan na kawo ƙarshen yaƙin, yana mai kiransa "abin da ba za a lamunta ba kwata-kwata."