| Hausa
GABAS TA TSAKIYA
2 minti karatu
Fidan ya yi gargadi kan amfani da Mashigar Teku ta Hormuz a matsayin makami a rikicin yankin
Ministan Harkokin Waje Hakan Fidan ya yi gargadin cewa tangarda ga hanyar na yin barazana ga zaman lafiyar yankin da tattalin arzikin duniya.
Fidan ya yi gargadi kan amfani da Mashigar Teku ta Hormuz a matsayin makami a rikicin yankin
Fidan ya ce dole ne rikicin da ake ci gaba da yi a yankin Gulf ya zama bai janyo a manta da batun Gaza ba / AA / AA

Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan a ranar Talata ya ce ‘Kar Mashigar Teku ta Hormuz ta zama makami, yana mai gargadin cewa tangarda ga hanyar na yin barazana ga zaman lafiyar yankin da tattalin arzikin duniya.

Da yake jawabi a wani taron manema labarai na hadin gwiwa da Firaministan Qatar kuma Ministan Harkokin Waje Mohammed bin Abdulrahman bin Jassim Al Thani a Doha, Fidan ya kuma ce ya zama lallai a tabbatar da tashin hankalin da ke ci gaba da faruwa a yankin Gulf "ba zai sa a manta da batun Gaza ba."

Ya kuma yi gargadin cewa fadadar Isra'ila na ci gaba da zama babbar barazana ga "kwanciyar hankali da tsaro" na yankin.

Al Thani ya ce Qatar da Turkiyya suna goyon bayan kokarin shiga tsakani na Pakistan da nufin kawo karshen yakin Amurka-Isra'ila kan Iran da kuma sake bude mashigar Hormuz, yana mai jaddada bukatar dawo da kwanciyar hankali da kuma tabbatar da 'yancin zirga-zirga ta hanyar mai matukar muhimmanci.

"Qatar da Turkiyya sun goyi bayan kokarin shiga tsakani na Pakistan don kawo karshen yaki kan ran da sake bude mashigar teku ta Hormuz," in ji shi.

Ministan Harkokin wajen Qatar ya kuma ce bai kamata Tehran ta yi amfani da hanyar ruwa a matsayin hanyar "zalunci ko cin zarafi" ga kasashen Gulf ba.

Da yake jawabi kan Gaza, Al Thani ya zargi Isra'ila da ci gaba da keta yarjejeniyar tsagaita wuta da kuma "amfani da tallafin jinkai a matsayin makami" a yankin.

An yi taron manema labarai na hadin gwiwa a yayin ziyarar aiki da Fidan ya kai Doha babban birnin Qatar.

Rumbun Labarai
Iran ta mayar da martani ga masu shiga tsakani na Pakistan kan shawarar Amurka ta kawo ƙarshen yaƙi
Saudiyya ta musanta zargin bayar da izinin amfani da sararin samaniyarta don ayyukan soja
Iran ta harba makamai masu linzami ga sojin Amurka bayan hari kan tankar dakon manta
Darussa daga sabon tsarin tafiyar da duniya: Ba za a iya sayen tsaro ba, amma dole a gina shi
Trump ya dakatar da shirinsa na taimaka wa jiragen ruwa wucewa ta Mashigar Hormuz
Shugabannin duniya na matsa wa Iran lamba yayin da ake fargabar batun tsagaita wuta zai iya rushewa
Harin da Amurka ta kai Mashigar Hormuz ya kashe fararen-hula 5, a cewar Iran
Iran ta ce duk wani shirin Amurka kan mashigar Hormuz zai zama keta yarjejeniyar tsagaita wuta
Iran ta ba Amurka wata guda don janye toshe tashoshin ruwanta da kawo ƙarshen yaƙin Iran da Lebanon
Buɗaɗɗiyar maƙabartar Gaza: Gawawwaki 8,000 sun maƙale, yayin da aikin kwashe ɓaraguzai ya tsaya cak
Iran ta kunna na'urar tsaron sama yayin da Trump ke fuskantar wa'adin ikon shiga yaki daga Majalisa
Isra'ila na rasa goyon bayanta a tsakanin matasa 'yan  Amurka - Rahoto
Za a ci gaba da tattaunawa tsakanin Amurka da Iran ta waya – Trump
Trump ya ce bai kamata Iran ta samu makamin nukiliya ba a liyafar da aka shirya wa Sarki Charles III
Netanyahu ya bayyana a kotu don shari'ar cin hanci da rashawa a karon farko tun soma yaƙin Iran
Rikicin Gabas ta Tsakiya na koyar da darasi: Turkiyya ta zama kan gaba a zaɓin ƙasashen Afirka
Trump bai yarda da tayin Iran na sake buɗe Mashigar ruwan  Hormuz ba, in ji rahotanni
Mene ne Tehran ke gabatarwa domin kawo ƙarshen yaƙin Amurka da Isra'ila a kan Iran?
Araghchi ya faɗaɗa zirga-zirgar diflomasiyyar Iran daga Islamabad zuwa Moscow
Sisi na Masar ya yi gargaɗi kan 'ƙoƙarin da ake yi da gangan' na sake zana taswirar Gabas ta Tsakiya