Fararen-hula biyar aka kashe a wani harin Amurka kan ƙananan jiragen ruwa na jigilar kayayyaki a mashigar ruwan Hormuz, kamar yadda kafofin watsa labaran Iran suka ruwaito ranar Talata, inda suka musanta labarin da Washington ta bayar game da aukuwar lamarin.
Kamfanin dillancin labaran Tasnim da Iran ke da ƙwarya-ƙwaryar iko a kansa, ya ambato wata majiyar tsaro da ta ce wani bincike ya gano cewa dakarun Amurka sun kai hari kan ƙananan jiragen ruwa biyu ɗauke da kayayyaki daga Khasab a gaɓar tekun Oman zuwa ta Iran.
“Biyo bayan iƙirari na ƙarya da Amurka ta yi cewa ta kai hari kan ƙananna jiragen ruwa 6 na Iran, tun da babu wani jirgin ruwan yaƙi na IRGC [rundunar juyin juya halin Iran] da aka afka wa, an gabatar da bincike game da iƙirarin ta hanyar majiyoyi na yankin,” kamar yadda aka ambato majiyar tana cewa.
Fararen-hulan da aka kashe a harin fasinjoji ne a kan ƙananan jiragen ruwa, in ji majiyar ta soji, tana mai bayyana harin a matsayin wani mataki “na gaggawa” da “fargabar” Amurka kan ayyukan ƙananan jiragen ruwan IRCG ta haddasa.
Daga farko dai hedkwatar tsaron Amurka (CENTCOM) ta ce an yi amfani da helikwaftocin Amurka wajen lalata “ƙananan jiragen ruwan Iran da ke barazana ga jigilar kayayyaki ta ruwa na ‘yankasuwa,” tana mai cewa an kai hari kan jiragen ruwan ne domin tabbatar da tsaro kan kaikomon jiragen ruwa a muhimmiyar hanyar ruwan .
CENTCOM ta kuma zargi Iran da buɗa wuta kan jiragen ruwa na yaƙin Amurka da kuma jiragen ruwa na ‘yankasuwa ranar Litinin.
Rikicin na yanki ya fara ne lokacin da Amurka da Isra’ila suka ƙaddamar da hare-hare kan Iran ranar 28 ga watan Fabrariru, lamarin da ya janyo ramuwar gayya daga Tehran kan Isra’ila da kuma ƙawayen Amurka a cikin ƙasashen Labawan da ke gaɓar teku tare da rufe mashigin ruwan Hormuz.
Yarjejeniyar tsagaita wuta ta fara aiki ranar 8 ga watan Afrilu ta hanyar shiga tsakani na Pakistan, amma tattaunawa a Islamabad ta gaza samar da fahimtar juna ta dindindin.
Daga baya, Shugaban Amurka Donald Trump ya tsawaita tsagaita wutar ba tare da wa’adi ba.
Tun ranar 13 ga watan Afrilu ne Amurka ta ƙaƙaba ƙawanya ta sojin ruwa a mashigar ruwan Hormuz.





