| Hausa
GABAS TA TSAKIYA
3 minti karatu
Shugabannin duniya na matsa wa Iran lamba yayin da ake fargabar batun tsagaita wuta zai iya rushewa
Shugabannin duniya sun bukaci Iran ta ci gaba da tattaunar diflomasiyya bayan sabbin hare-hare sun tilasta dakatar yarjejeniyar tsagaita wuta tare da kara ta'azzara tashin hankali a mashigin Hormuz.
Shugabannin duniya na matsa wa Iran lamba yayin da ake fargabar batun tsagaita wuta zai iya rushewa
Shugabannin duniya na matsa wa Iran lamba yayin da ake fargabar batun tsagaita wuta zai iya rushewa / Reuters

Shugabannin duniya suna matsa wa Tehran lamba a ranar Talata kan ta koma tattaunar diflomasiyya don kawo karshen yakin Gabas ta Tsakiya, bayan hare-hare da dama da aka kai a yankin wanda ya rushe batun tsagaita wuta.

Yunkurin sake sabunta tattaunawar ya biyo bayan musayar wuta tsakanin Iran da Amurka a kan Mashigar Hormuz, yayin da kawar Washington wato Hadaddiyar Daular Larabawa ta ba da rahoton hare-haren Iran a karon farko tun bayan da aka ayyana tsagaita wuta kusan wata guda da ya wuce.

Kokarin cim ma matsaya ta diflomasiyya tsakanin Washington da Tehran ya tsaya cak tun bayan tsagaita wuta, inda har sau biyu Amurka ta soke shirin tura manyan jami'ai zuwa tattaunawa a Pakistan.

Tehran ta sha alwashin ba za ta miƙa ikonta a kan mashigar tekun Hormuz ba - wata ƙaramar hanyar ruwa da ake ratsa wa kashi ɗaya bisa biyar na jigilar man fetur din duniya kafin Amurka da Isra'ila su kai wa Iran hari a ranar 28 ga Fabrairu.

Shugaban gwamnatin Jamus Friedrich Merz ya roƙi Tehran da ta "koma kan teburin tattaunawa ta daina wahalar da yankin da duniya baki daya," yana mai nanata kiran shugaban Faransa Emmanuel Macron da Firaiministan Birtaniya Keir Starmer.

Saudiyya, babbar kawar Amurka wacce Iran ta kai wa wauraren makamashinta hari, ta bi sahun wannan kiran a ranar Talata inda ta bukaci a dakatar da tashin hankalin tare da neman a kara "ƙoƙarin da ake na diflomasiyya don cimma mafita ta siyasa".

A ranar Litinin Amurka ta ce dakarunta sun nutsar da aƙalla ƙananan jiragen ruwan Iran guda shida, amma Iran ta musanta batun inda ta ce an kai hari kan wani jirgin ruwan yaƙinta kuma ta zargi Washington da kashe fararen hula biyar a cikin jiragen ruwa.

‘Munanan hare-hare’

Hadaddiyar Daular Larabawa UAE, wacce abokiyar Amurka ce ta kud da kud, ta ce an kai mata hari da makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuƙa daga Iran, tana mai kiran hakan da "munanan hare-hare da kuma keta doka da ba za a yarda da ita ba".

Wani hari da aka kai kan wani wurin samar da makamashi a masarautar Fujairah ya jikkata 'yan ƙasar Indiya mutum uku, a cewar hukumomin UAE.

Sun ce an harba makamai masu linzami har guda huɗu, inda aka harba uku cikin nasara, yayin da ɗayan ya faɗa cikin teku.

Kazalika Iran ta harba jiragen sama marasa matuƙa kan wani tankar dakon mai da ke da alaƙa da kamfanin mai na ƙasar UAE ADNOC, a cewar Hukumomin.

Wani babban jami'in sojin Iran bai musanta harin ba, amma ya ce Iran ba ta da ‘‘wani shiri da aka riga aka tsara don kai hari kan wuraren mai da ake magana a kai’’.

"Abin da ya faru ya samo asali ne daga kasadar sojojin Amurka na ƙirƙirar wata hanya don jiragen ruwa su ratsa ta mashigar Hormuz ba tare da izini ba," kamar yaada jami'in ya fada ta gidan talabijin din gwamnati.

"Dole sojojin Amurka su ɗauki alhakin abin da ya faru."

Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araghchi ya ce rikicin ya nuna cewa babu "mafita ta soji a rikicin siyasa" kuma ya nuna ƙoƙarin Pakistan na ci gaba da shiga tsakani.

"Ya kamata Amurka ta yi taka tsantsan kada masu son zuciya su mayar da ita cikin wani mummunar yanayi. Don haka idan UAE ta bukaci ‘yanci ba shi da wani tasiri,’’ kamr yadda ya rubuta a shafinsa na X.