Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida da Tsaro ta Nijar ta gabatar da wani sabon daftarin dokar sake fasalin rabon yankunan ƙasar, wanda zai ƙara adadin jihohin Nijar daga takwas zuwa 19.
Kamfanin dillancin labaran ƙasar, ANP ya ruwaito cewa shirin ya kuma tanadi ƙirƙirar sabbin ƙananan hukumomi 20 domin ƙarfafa kasancewar gwamnati a faɗin ƙasar da kuma inganta shugabanci a matakin ƙananan hukumomi.
A cewar gwamnatin ƙasar, sabon tsarin zai taimaka wajen bunƙasa tattalin arziki da walwalar jama’a, tare da inganta ayyukan tsaro da gudanar da harkokin gwamnati bisa la’akari da ƙalubalen tsaro da ci gaban al’umma.
Wannan sauyi na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin mulkin sojin Nijar ke ci gaba da aiwatar da sauye-sauye a tsarin mulki da gudanarwar ƙasar tun bayan hambarar da gwamnatin farar hula a watan Yulin 2023.
Bisa ga sabon tsarin, jihohin Agadez da Diffa da Dosso za su samar da jihohi biyu-biyu, yayin da jihohin Maradi da Tahoua da Tillabéri da Zinder kowacce za ta samar da jihohi uku. Sai dai Yamai ce kaɗai za ta ci gaba da kasancewa jiha guda ɗaya.
Baya ga ƙirƙirar sabbin jihohi, gwamnatin Nijar ta kuma sauya sunayen tsoffin jihohi takwas na ƙasar.
A ƙarƙashin sabon tsarin:
• Diffa za ta koma Komadougou
• Zinder za ta koma Damagaram
• Maradi za ta koma Katsina
• Dosso za ta koma Ziggui
• Tillabéri za ta koma Issa
• Agadez za ta koma Abzine
• Tahoua za ta koma Ader
Sai dai Yamai ce kaɗai za ta ci gaba da amfani da tsohon sunanta.
Sauran sabbin jihohin da za a ƙirƙira sun haɗa da Kawar da Mangari da Arewa da Tazar da Gobir da Azawak da Magia da Tougana da Kourfey da Daoura da Damergou.
Wasu daga cikin sababbin sunayen jihohin sun samo asali ne daga tsoffin masarautu da yankunan tarihi da suka yi fice a Nijar tun kafin mulkin mallaka.
Haka kuma, daftarin dokar ya tanadi ƙirƙirar sabbin manyan biranen jihohi 15 da kuma sabbin ƙananan hukumomi 20, ciki har da Tabelot da Djado da Chétimari da Dogon Kiria da Guéchémé da Sambéra da Tibiri da Ourafane da Kornaka da Kanambakaché da Hamdallaye da Bambèye da Kaou da Ourno da Tamaské da Goroual da Makalondi da Kellé da Gangara da Guidimouni.
Rahoton ya ce sabbin ƙananan hukumomin za su rabu tsakanin jihohin ƙasar daban-daban, inda Maradi da Tahoua za su samu huɗu-huɗu, Dosso da Zinder uku-uku, Agadez da Tillabéri biyu-biyu, yayin da Diffa da Yamai za su samu guda ɗaya kowacce.
Wannan sauyi na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin mulkin sojin Nijar ke ci gaba da aiwatar da sauye-sauye a tsarin mulki da gudanarwar ƙasar tun bayan hambarar da gwamnatin farar hula a watan Yulin 2023.
Nijar dai na fama da hare-haren ‘yanta’adda musamman a yankunan Tillabéri da Diffa da Tahoua, lamarin da hukumomi ke cewa sabon tsarin gudanarwa zai taimaka wajen ƙara kusantar gwamnati da jami’an tsaro zuwa yankunan karkara.
Masu lura da al’amura na ganin sauyin na daga cikin manyan gyare-gyaren tsarin gudanarwa da Nijar ta yi cikin shekaru da dama.













