Nijeriya, wadda ita ce ƙasar Afirka wadda ta fi samar da man fetur ta nemi shiga Hukumar Makamashi ta Duniya (IEA) a matsayin ƙaramar memba, in ji daraktan gudanarwa na IEA Fatih Birol a ranar Laraba.
"Na yi farin ciki da karɓar buƙatar Gwamnatin Nijeriya a hukumance a cikin wata wasiƙa daga Minista Ekperikpe Ekpo na neman Nijeriya ta shiga dangin IEA a matsayin memba," kamar yadda Birol ya rubuta a shafinsa na X.
ZA KU SO WAƊANNAN
Hukumar IEA mai mambobi 32 a ranar Laraba ta bayyana cewa man da ake samarwa ba zai wadaci duniya a bana ba saboda yaƙin Iran ya shafi samar da man fetur ɗin a Gabas ta Tsakiya.
Nijeriya wadda ke samar da aƙalla ganga miliyan 1.4 a kowace rana, ita ce ƙasar Afirka wadda ta fi samar da man fetur a duniya.









